Kylian Mbappe ya zama dan wasan Paris Saint-Germain da ya fi zura kwallaye a tarihin babbar gasar tamaula ta Faransa wato Ligue 1.
Dan wasan mai shekaru 24 ya riga ya karya tarihin zura kwallaye a kungiyar a watan da ya gabata, lokacin da ya wuce Edinson Cavani, wanda ya ci wa PSG kwallaye 200 tsakanin 2013 da 2020.
- Barcelona ta raba maki karo na hudu a La Liga a bana
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Karasa Zaben Gwamnan Adamawa A Abuja
Amma har zuwa karshen wannan makon, Cavani ya kasance wanda ya fi zura wa PSG kwallo a gasar Ligue 1.
Sai dai hakan ya sauya a minti 31 da soma wasan da PSG ta doke Lens da ci 3-1 a ranar Asabar lokacin da Mbappe ya yi wa kungiyar rajistar kwallonsa ta 139 a gasar Ligue 1.
Yanzu dai Cavani ne na biyu a jerin wanda ya zura kwallaye 138 a gasar Ligue 1, yayin da Zlatan Ibrahimovic ke matsayi na uku da kwallaye 113.
Kylian Mbappe ne ya fara cin kwallo a wasan kuma na 139 a wasa 169 da ya yi wa kungiyar.
Lens ta karasa karawar da ’yan wasa 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Salis Abdul Samed jan kati minti 19 da take leda.
Sauran da suka ci wa PSG kwallayen sun hada da Lionel Messi da kuma Vitinha, yayin da Lens ta zare daya a bugun fenariti ta hannun Przemyslaw Frankowski.
PSG mai fatan lashe Ligue 1 na 11 tana ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Faransa ta bana da maki 72.
Lens mai maki 63 ce ta biyu, sai Marseille ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Lens.
Paris St Germain za ta ziyarci Angers ranar Juma’a 21 ga watan Afirilu, domin buga wasan mako na 32 a Ligue 1.