✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayukan da ke magance nankarwa

Nankarwa na nufin yaushin fatar jiki ko yaushin fatar nono bayan haihuwa. Tana uzura wa mata har ta sanya mazajensu su rika kyamar su. Nankarwa…

Nankarwa na nufin yaushin fatar jiki ko yaushin fatar nono bayan haihuwa. Tana uzura wa mata har ta sanya mazajensu su rika kyamar su. Nankarwa tana saurin tsufar da fata, ta sanya ta jemewa ko kodewa. Don haka a wannan makon na kawo miki bayanin yadda za ki magance ta. Ga bayanin yadda za ki magance nankarwa:.

–    Ki rika shafa man cod liber oil ko man bitamin E Oil ko man zaitun a wurin da ke da nankarwa, sannan ki rika goge wurin da yatsunki zuwa wani dan lokaci, idan kika juri hakan za ki rabu da nankarwa.
–    Ki rika motsa jikinki, domin motsa jiki na sanya fata ta mike, hakan zai taimaka ki magance nankarwa.
–    Shafa man kade zai taimaka wajen rage kaikayin nankarwa.
–    Cin abinci mai dauke da mabambantan sinadarai na magance nankarwa.
–    Ki rage shan shayi mai sinadarin ‘caffein’, domin sinadarin caffeine na haifar da nankarwa
–    Shafa man Labender oil zai magance nankarwa.
Bin wadannan hanyoyin da na lissafo a sama zai taimaka miki wajen magance nankarwa ba tare da kashe kudi mai yawa wurin sayan mayuka ba. Za ki iya amfani da wadannan hanyoyi ba wai sai kina fama da nankarwa ba. Yin hakan zai sanya fatarki ta rika sheki da haske da danshi da kuma laushi.a samu canji, domin gashin zai zama mai sheki da santsi da laushi da kuma tsayi.