✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayar da shirin afuwa ga ’yan Neja-Delta saniyar tatsa

Tsohon Shugaban kasa marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ne ya kaddamar da shirin afuwa ga tsagerun Neja-Delta cikin shekarar 2009 bisa kyakkyawar manufar a kawo karshen…

Tsohon Shugaban kasa marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ne ya kaddamar da shirin afuwa ga tsagerun Neja-Delta cikin shekarar 2009 bisa kyakkyawar manufar a kawo karshen fasa bututun mai da kuma tayar da kayar bayan da tsagerun ke yi, inda aka bukaci su mika makamansu don su samu gwaggwaban lada.
A tun asalin tsarin shirin, an yi kyakkyawan tanadi mai fadi da kuma inganci wajen inganta rayuwar ’yan kungiyar MEND da suke ikrarin fafutikar kwato ’yancin Neja-Delta. An shirya idan suka mika makamansu za a ba su damar taka rawa a bangaren inganta tattalin arziki da kuma harkokin siyasa a yankin Neja-Delta da kuma kasa baki daya.
An ce za a gudanar da shirin afuwar na wadansu watanni ne, inda daga nan gwamnati za ta dauki doka hade da hukunta  wadanda suka ki mika makamansu ko suka ci gaba da fasa bututun mai ko suka ki yarda da shirin afuwar.
Wannan shirin na marigayi ’Yar’aduwa ya samu karbuwa a wurin ’yan kasa da ma duniya baki daya, domin hakan ya nuna durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne, wato gwamnati ta yi haka ne don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, kasancewar a zahirin gaskiya ba daidai ba ne gwamnati ta nemi sulhu da wadanda suka dauki makamai suke yakar kasa ta hanyar kashe jami’an tsaro da fararen hula, suka rika tayar da bama-bamai a gine-ginen jama’a ko na gwamnati ba kawai a yankin Neja-Delta ba har a sauran sassan kasar nan. Duk da haka aka yi sulhu da su aka kuma samar musu da ayyukan yi, wadansu kuma aka tura su makarantu a nan Najeriya da kasashen waje.
Sai dai bayan mutuwar ’Yar’aduwa a shekarar 2010, sai shirin ya canza salo, inda aka rika ware kudi mai yawa a kan shirin, aka kuma manta da cewa wannan shirin na lokaci kankane ne, wanda hakan yake nuna wannan shirin ya zama shiri na dindindin.
Akwai matsaloli masu yawa dangane da wannan shirin afuwar a yanzu haka.
Matsala ta farko ita ce, tun bayan rasuwar ’Yar’aduwa fadar shugaban kasa ce ke kula da shirin afuwar, inda take nada mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kan shirin, sannan ta dora masa alhakin gudanar da wadansu ayyuka, wanda ya sanya kudin da ya kamata a yi wa jama’a aiki ke zurarewa ba tare da an ga amfaninsa ba. Matsala ta biyu ita ce, babu cikakken bayanin yadda ake kashe kudin don gudanar da shirin da a yanzu ake kira Shirin Afuwar Shugaban kasa (PAP).
Matsala ta uku ita ce, an fitar da kudi ba kuma tare da an ga wani abu a kasa ba, wanda hakan ya kawo wa baital-malin gwamnati gibi har Babban Bankin Najeriya ya bayyana halin da ake ciki dangane da shirin afuwar PAP.
A wata takarda da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi ya gabatar yayin taron matasa na kasa a Jihar Abiya ya ce, shirin afuwar PAP ya lashe Dala biliyan 1.
Shugaba shirin PAP, Mista Kingsley Kuku, wanda kuma shi ne mai ba shugaban kasa shawara kan Ma’aikatar Neja-Delta a ranar Litinin da ta gabata ya ce, daga shekarar 2010 zuwa wannan shekarar an ba shirin afuwar Naira biliyan 223.133 ba Naira biliyan 400 da ake ta yayatawa ba.
A zahirin gaskiya kudin zai iya fin haka idan aka yi la’akari da cewa Ma’aikatar Neja-Delta da Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta suna ba shirin afuwar gwaggwabar gudunmuwa, wanda kuma kai-tsaye suke tura kudin ofishin shirin afuwar.  Matsala ta hudu kuma ita ce, ana amfani da kudin wajen ba wadanda suke maganganun a kafafen yada labarai don su yi shiru.
Mista Kingsley ya tabbatar da hakan inda ya ce, idan har ana so a kawo karshen fasa bututun mai da kuma satar mai sai Hukumar Kamfanin Mai ta Najeriya (NNPC) ta dauki tsofaffin tsagerun aiki. Tabbas wannan babbar dabara ce a ba kura ajiyar nama, amma abin da muke so a sani shi ne, har yanzu makudan kudaden da ake warewa don shirin afuwar bai haifar da da mai ido ba.
An rika daga lokacin da ya kamata a kawo karshen shirin afuwar, wanda a yanzu Mista Kuku ya fara shirye-shiryen ganin an daga lokacin kammala shirin zuwa 2017. Wannan shirin ya dauki lokaci ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba, don haka lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen wannan shirin.