Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da zargin cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin mayar da Nijeriya kan tsarin ƙasa da ke kan tafarkin jam’iyya ɗaya a ƙarƙashin mulkinsa.
Shugaban ya kore wannan zargin ne a yayin jawabin da ya yi na zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, yau Alhamis.
- Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
- 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya
Tinubu ya ce masu tunanin cewa APC na son mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya, to tunanin nasu kuskure ne, kuma suna yin sa cikin ruɗani ne.
Ya ce: “Tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu. Kuma ba zai taɓa zama cikin manufofinmu ba.”
Sai dai shugaban ya ce wannan ba zai hana jam’iyyar APC yin maraba da duk wanda ke son shiga cikinta ba.
“Zai kasance mun yi maguɗin siyasa idan muka hana mutane daga wasu jam’iyyun siyasa shigowa jam’iyyar APC,” in ji Tinubu.
Sai dai Tinubun ya ce suna farin cikin da rikicin ci gida da ke addabar jam’iyyun adawa kuma ba zai shawarar yadda za su warware matsalolinsu ba.
“Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa a cikin ruɗani, saboda hakan nasara ce bangarenmu.
“Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba, batun jam’iyya ɗaya bai ta taso ba, amma siyasar za ta taɓarɓare idan muka rufe ƙofa ga masu son shiga APC,” in ji shi.