✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Kurdawa sun kama ’yan IS 125 a Syria

Dakarun Kurdawa sun ce sun kame wasu mutane 125 da ake zargin ’yan kungiyar IS ne a wani bangare na aikin tsaro a sansanin ’yan…

Dakarun Kurdawa sun ce sun kame wasu mutane 125 da ake zargin ’yan kungiyar IS ne a wani bangare na aikin tsaro a sansanin ’yan gudun hijirar da ke Arewa maso gabashin Syria a ranar Juma’a.

Dakarun Syrian da ke samun goyon bayan Amurka (SDF) sun ba da sanarwar kaddamar da wannan samame a ranar Lahadin da ta gabata kan ’yan na IS a cikin matsugunin, inda aka yi kashe-kashe sama da 40 tun farkon shekarar nan.

Hukumomin Kurdawa sun yi gargadin cewa sansanin, wanda yake da kusan mutane 62,000, yana zama tamkar maboyar masu tsattsauran ra’ayi kasancewa mayakan IS na buya a tsakanin mazauna sansanin.

“Mun kame ’yan IS ciki har da kwamandoji 20 masu kula masu kisan gilla a sansanin,” inji Ali al-Hassan, mai magana da yawun jami’an tsaron Kurdawan na Asayish.

An yi kashe-kashe sama da 47 tun farkon shekarar, inji Hassan.

Da yake magana a hedikwatar Asayish da ke garin Al-Hol, ya ce mambobin kungiyar IS da dama sun kutsa cikin sansanin ta hanyar batar da sawu kamar fararen hula da suka rasa muhallansu.

“Burinsu shi ne su yi aiki a ciki kuma su sake haduwa,” inji Hassan.

Ya kara da cewa yayin yakin, Asayish din sun gano “na’urorin tayar a ababen fashewa” da wasu kayan aikin soji.