Akalla sojoji uku ne suka mutu, wasu hudu kuma sun samu rauni a wata arangama da suka yi da mayakan ISWAP da Boko Haram.
Da yake ganawa da manema labarai, kakakin Rundunar Sojin Najeriya Birigediya Janar Benard Onyeuko, ya ce rundunar ta rasa sojoji uku.
- Yadda na kubuta daga hannun Boko Haram – ’Yar shekara 13
- Mayakan ISWAP sun kashe sojoji tara a Borno
- ISWAP ta yi garkuwa da daruruwan mutane
- Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da dama a Borno
“Ina jimamin sanar da cewa mun rasa jami’ai uku, hudu daga cikin wadanda suka ji rauni an debo su zuwa asibitin sojoji domin ci gaba da kula da su”, inji Onyeuku.
Ya ce bayan musayar wuta na tsawon lokaci, sojojin sun yi nasarar kora ’yan tada kayar bayan, sannan an kwato makamai da dama da suka hada da bindigogi, harsasai daga masu tayar da kayar bayan.