Rahotanni daga Karamar Hukumar Chibok da ke Jihar Borno na cewa mayakan Boko Haram sun sace ’yan mata da dama a wani sabon hari da suka kai yankin.
Wani mazaunin yankin ya ce mayakan sun kutsa kai garin ne da daren Alhamis inda suka rika harbe-harbe ta ko ina.
Lamarin dai ya tilasta wa fararen hula suka rika guduwa zuwa cikin dazuka kauyen Pemi, wanda ke kusa da garin na Chibok domin neman mafaka.
Kazalika, mayakan sun kuma banka wa gine-gine akalla 20 wuta a garin, ciki har da gidaje da wata majami’a.
Wani mazaunin yankin, Bitrus Yohanna, ya ce ’yan sa-kai da ke yankin maharan suka fi yunkurin kai wa farmakin.
“Rana ce mai cike da bakin ciki a gare mu mutanen Pemi, maharan sun zo da tarin yawa, sannan suka fara ruwan wuta.
“Sun kama kwamandanmu na ’yan sa-kai suka yi masa yankan rago, sannan suka kone gidaje da dama da wata majami’a,” inji Bitrus.
Shi ma wani mai aikin sa-kai a yankin, Ba’ana Musa, wanda ke aiki tare da mafarautan yankin, ya ce takwas daga cikin wadanda aka kama din sun tsere, amma an gudu da mutum 17.
“Mun damu matuka da satar wadannan ’yan matan. Maganar da nake da kai yanzu haka, akwai akalla su 17 a hannunsu.
Garin Chibok dai ya yi tambari ne a shekarar 2014, lokacin da maharan na Boko Haram suka sace dalibai ’yan mata kimanin 276 a sakandiren garin.
Ko da yake an ceto da dama daga cikinsu, wasu kuma sun kubuta, har yanzu akwai sama da mutum 100 da ba a san inda suka shiga ba.