✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawaki ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da wasa a dandali a Afirka ta Kudu

Ya yanke jiki ya fadi lokacin da yake tsaka da waka a dandali

Wani fitaccen mawaki a Afirka ta Kudu, Costa Tsobanoglou, ya yanke jiki ya fadi lokacin da yake tsaka da wasa a dandali a birnin Johannesburg na kasar.

Mawakin, wanda rahotanni suka nuna ya yanke jiki ya fadi a bikin wasa na Ultra Music Festival ranar 11 ga watan Maris din 2023 daga bisani dai ya ce ga garinku nan.

Wanda aka fi sani da Costa Titch, mutuwar fitaccen mawakin ta zo ne ’yan makonni bayan shi ma wani fitaccen mawakin gambarar zamanin nan, Kiernan Jarryd Forbes, an harbe shi birnin Durban.

A wani bidiyo dai da ya karade gari, an fa mawakin ya fadi a kasa, amma ya ci gaba da wakar lokacin da yake kasa.

Daga bisani dai dogarinsa ya sake tayar da shi amma ya sake faduwa a karo na biyu, lamarin da ya tilasta dole aka janye shi daga kan dandali.

An haifi marigayin ne a garin Nelspruit da ke Jihar Mpumalanga na kasar a shekarar 1995, kuma ya yi fice da wasu wakokinsa kamar su Nkalakatha da Activate da kuma Big Flexa.

Wani mai sharhi kan al’amuran shakatawa, Phil Mphela, ne ya tabbatar da mutuwar mawakin a shafinsa na Twitter, inda ya wallafa cewa, “Allah Ya kyauta makwanci Costa Titch. Mawakin kuma mai rawa haifaffen Nelspruit ya rasu yana da shekara 27.”

Tuni dai mutane a ciki da wajen kasar suka shiga mika sakonnin ta’aziyyarsu ga iyalai da ’yan uwan mamacin.