✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawaki Umar M. Shareef ya zama jakadan gidan talabijin na Qausain

Gidan Talabijin na Qausain ya nada Shahararren Mawaki Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna.

Gidan Talabijin na Qausain ya nada Shahararren Mawaki Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna.

Shugaban Rukunin Kamfanin Qausain, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a yayin kaddamarwar  da  gidan talabijin din ya shirya a harabar ofishinsa da ke Titin Sultan,  a birnin Kaduna a wannan makon.

Shugaban Kamfanin ya bayyana jin dadinsa tare da mika godiyarsa ga Allah da kuma ilahirin ma’aikata da wadanda suka bayar da gudunmuwa har gidan talabijin ya tabbata.

Malam Nasir ya bada tabbacin cewa gidan talabijin din zai tafi daidai da zamani kamar sauran manyan gidajen talabijin na duniya, tare da kare dukkan wani hakkin da ya rataya a wuyansa na ganin ya samar da ingantattun bayanai da nagartaccen ilmantarwa domin amfanin al’umma baki daya.

Shi ma a nasa jawabin, Babban Daraktan Qausain, Alhaji Musa H. Isa, ya bayyana cewa sun samar da tashar Qausain TV ne daidai da zamani da kuma bin ka’idoji na samar da ingantaccen gidan talabijin.

Musa, ya kuma gabatar da fitattacen Mawaki Umar M Shareef a matsayin jakadan tashar ta Qausain TV.

Shi ma mawakin ya bayyana jin dadinsa tare da alkawarin kawo cigaba mai dorewa a matsayinsa na jakadan tashar.

Tun da farko a tsokacinsa, Babban Manajan tashar, Umar Faruk Adam, ya nemi goyon baya daga al’umma da ganin sun mara wa gidan tashar baya ta fuskar karfafa gwiwa da kuma kawo tallace-tallace.

Ya kara da cewa sun samar da hanya mai sauki ga masu sha’awar sanya hannun jari ko son kulla alakar kasuwanci da gidan talabijin din na Qausain TV.