✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mawaki Kanye West zai kaurace wa barasa da jima’i tsawon wata daya 

Kanye West zai yi azumin shan barasa da jima'i na wata guda.

Shahararren mawakin nan na Amurka, Kanye West, ya ba da sanarwar fara hutun wata daya na kaurace wa barasa da jima’i da sauran abubuwa don neman tsarkake kansa.

Mawakin ya ba da sanarwar hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

Kanye West wanda kuma ake kira da Ye, yana shan suka saboda kalaman kyamar Yahudawa da ya yi a baya-bayan nan, lamarin da ya kai shi ga rasa dimbin dukiya.

Kalaman nasa sun janyo kamfanin Adidas janye harkallar miliyoyin dala da suka kulla da shi a baya.

A cikin sakon da ya wallafa, mawakin ya lissafo abubuwan da zai rika yi yayin hutun kwana 30 da ya dibar wa kansa, ciki har da kin yin magana da kowa, babu shan barasa, babu kallon fina-finan batsa da sauransu.