Mawaki kuma jarumi a masana’antar fina-finan Kudancin Najeriya ta Nollywood Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W, ya lashe zaben fid-da gwanin jam’iyar PDP a karo na biyu.
Jarumin dai na takarar kujerar dan majalisar Jiha mai wakiltar mazabar Eti-Osa ne a Legas, kuma tun a zaben farko da aka gudanar ranar 22 ga watan Mayu a Jihar ya samu nasara, sai dai sunansa ya yi baton dabo a jerin sunayen na karshe.
- Fitar da dan takara: Gwamnonin APC sun mika wa Buhari sunan mutum 5
- Ya maka Hadiza Gaban a gaban kotu saboda ta ki auren shi
Kwamitin Gudanarwar jam’iyar na kasa dai ya soke zabukan da aka gudanar a mazabu 24 na kasar nan, in da ya ce a sake su a jiya.
Zaben dai na jam’iyar ya zo da rudani a mazabu 24 daga ‘ya’yan jam’iyyar.
A hannu guda kuma, ana ci gaba da gudanar da zabukan fid-da gwanin PDPn a wasu Kananan Hukumomin yayin hada wannan rahoton.
Banky W dai ya kara ne da masanin Shari’a, Mista Sam Aiboni, a zaben da aka gudanar a hedkwatar jam’iyar da ke titin Alpha Beach a Karamar Hukumar ta Eti-Osa.
An kuma fara shi ne da da karfe 4:45, kuma an kwashe dakiku 30 ana gudanar da shi tsakanin ‘yan takarar biyu, da kuma Daliget 28 daga mazabh, sai guda daga Tarayya.
A karshen zaben dai shugaban zaben Abayomi ya ce an yi cikin lumana kuma a bayyane.
Da yake bayyana farin cikinsa kan nasarar da ya samu, Banky W, ya yi godiya ga jam’iyyarsa, da kuma mutanen da suka ba shi damar a dama da shi a zaben 2023.
Babban kalubalen da zaben fid-da gwanin PDPn ke fuskanta a yanzu shi ne yadda ‘ya’yan jam’iyar ke bayyana damuwa kan rashin isassun bayanai akan zabukan.