✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mawaki 50 Cent zai shirya fim kan Hushpuppi

Mawakin Amurka kuma mai fitowa a fina-finai da shirin talabijin, Curtis Jackson, wanda aka fi sani da 50 Cent, zai shirya fim kan dan Najeriyar…

Mawakin Amurka kuma mai fitowa a fina-finai da shirin talabijin, Curtis Jackson, wanda aka fi sani da 50 Cent, zai shirya fim kan dan Najeriyar nan da ya shahara a shafin sada zumunta na Instagram, Ramon Abbas.

50 Cent ya bayyana cewa, zai soma shirin wani fim mai dogon zango kan Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi, dan damfarar nan da aka yanke wa hukuncin dauri na shekara 11.

Mawakin dai wato 50 cent na cikin jaruman da suka haska a fitaccen shirin fim din nan na Power da Power Book II, da Power Book III da dai sauransu.

A shafinsa na Instagram mawakin ya shaida wannan aniya tasa da ya ce nan bada jimawa ba za a soma nadar fim din, saboda ankarar da wasu aikata irin wannan muggan laifuka ta intanet.

Hushpuppi ya yi fice wajen nuna rayuwar da yake yi ta facaka a shafinsa na Instagram mai mabiya miliyan 2 da dubu 800, kafin a rufe shafin a kwanakin nan.

A farkon makon nan ne wata kotu a Amurka ta daure Hushpuppi sama da shekara 11 a gidan yari.

Alkalin kotun a Los Angeles da ya yanke wa Hushpuppi hukunci ya kuma umarce shi da ya biya dala $1,732,841 ta diyya ga wasu mutum biyu da ya damfara.

Bayanai daga kotun California sun ce, tun a watan Afrilun shekarar 2021 ne dai ya amsa laifin aikata almundahanar kudi, da yunkurin kwashe fiye da Dala miliyan 1.1 daga wani da ke kokarin ba da tallafi ga wata sabuwar makarantar yara a Qatar.

Mataimakin Daraktan da ke kula da rundunar tsaron FBI ta Los Angeles Don Alway, ya ce Hushpuppi dai ya yi fi ce ne a damfarar mutanen da suka fito daga kasashen duniya daban-daban musamman Amurkan.