✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawakan Hip-Hop na taimaka wa zaman lafiya – Young Gee

Gazali Sulaiman da aka fi sani da young Gee mawaki ne da ya kware wajen yin wakokin Hip-Hop. A cikin wannan tattaunawar da yayi da…

Gazali Sulaiman da aka fi sani da young Gee mawaki ne da ya kware wajen yin wakokin Hip-Hop. A cikin wannan tattaunawar da yayi da Aminiya ya bayyana dalilinsa na zaben yin wakokin hip-hop da kuma manufar da ya ke so ya cimmawa a harkar da ma sauran batutuwa da su ka shafi rayuwarsa.

Aminiya: Ka fara da gabatar mana da kanka?

An haife ni a garin Kafanchan a shekarar 1985 kuma a nan na taso na yi makarantar firamari har zuwa sakandiri daga nan kuma na wuce zuwa Kwalejin Ilmi ta tarayya da ke Zariya (F.C.E Zaria) inda na mallaki shaidar malanta ta kasa (NCE).

Daga nan kuma ban samu ci gaba ba sai na mayar da hankali na wajen bunkasa harkar wakokin da na ke yi har zuwa yau din nan.

Aminiya: Tun wanne lokaci ke nan ka fara waka kuma me ya ja ra’ayinka ga fara yin wakar Hip-Hop?

Toh, gaskiya zan ce na fara harkar waka ne tun shekarar 2006. Abin kuma da ya ja ra’ayina ya san a fara yin waka shi ne ganin yadda mawaki ke samun dama cikin sauki wajen isar da manufofin da ya ke son yadawa.

Idan muka dawo kan tambayarka kuwa sai in ce  na dauki salon wakar hip-hop ne a sakamakon yawan jin wakokinsu da na ke yi, wato ‘yan Hip-Hop na Amurka ke nan ta yadda ta kai ma ina haddace wakokinsu, to ganin haka ya sa na ce bari ni ma in fara gwadawa sai ga shi an wayi gari ni ma ina kirkirar nawa kuma in shiga dakin rera wakoki (Studio) in rera.

Aminiya: Zuwa yanzu ka rubuta wakoki kamar guda nawa, kuma ko ka samu damar fitar da wasu daga ciki?

Gaskiya ba zan iya kayyade su ba! Amma dai za su iya kai wa wakoki guda talatin amma wadanda na samu damar fitar da su za su kai guda goma ko fiye da haka.

Aminiya: Da wanne irin yare ka ke yi?

Wakokin Hip-Hop ka san su ai akwai na Hausa da na Turanci sannan akwai wadanda ake gwama harsunan duka ina yin su.

Aminiya: Ko kana da wata bakandamiya a cikin wakokin da ka yi?

Ka san ita bakandamiya mutane ne ke zaba. Ni a wajena kowace waka na yi bakandamiya ce. Amma a wajen mutane na ga sun fi son wakar ‘Smoking’ da kuma ‘Habba’, sune wakokina da mutane su ka fi magana a kai.

Aminiya: Ko ka taba samun wani alheri a sanadiyyar irin wadannan wakokin kasantuwar ba kowa ne ke sauraron wakokin Hip-Hop ba?

Alheri mai yawa ma kuwa! Na farko dai akwai kyaututtukan da na samu daga daidaikun mutane zuwa ’yan siyasa da jami’an gwamnati. Na biyu kuma na samu gogewa wajen iya sarrafa harshe da kuma mu’amala da mutane daban-daban. Akwai wasu kalomomi na Hausa da na Turanci wadanda sai a sanadiyyar waka ne na san ma’anoninsu har ta kai yanzu zan iya kirkiran labara in tsara sannan in bada umurnin wakoki.

Sannan akwai sanayya da na samu a sanadiyyar wannan harka ta waka wacce ta hada ni da mutanen da ban taba zato ba tun daga kan manyan mawaka da masu harkar kida da ’yan jaridu da sauransu.

Aminiya: Wanne irin kalubale ka fuskanta daga fara wadannan wakoki?

Akwai kalubale masu yawa da suka hada da rashin fahimta wacce ta kan kama tun daga gidanku har zuwa cikin al’ummar da kake rayuwa. Wasu za su rika ganin kamar ko hauka ka ke ko kuma rashin aiki yi ne ke damunka. Idan mun dawo ga masu sauraron wakokin Hip-Hop din kuma su matsalarsu shin e sun fi rinjaya ga sauraron kidan ne da bin sauti kawai ba wai ga sakon da kake isarwa a cikin wakar ba wannan ma ka ga kalubale ne sosai a wajen mawakan hip-hop. Sannan sai matsala ta karshe ba wai su ke nan ba; shi ne rashin cikakkun kayan aiki na zamani da kuma kwararrun makida hip-hop ta yadda sai mutum ya tashi zuwa Kano ko Kaduna ko Jos.

Aminiya: A karshe wanne kira ka ke da shi zuwa ga ’yan uwanka mawaka da kuma gwamnati?

Kirana ga mawaka shi ne mutum ya tashi ya taimaki kan shi da kan shi kada ya jira sai wani ya jagorance shi wajen fitar da wakokinshi ko wajen tallata su domin sai ka tashi tsaye Allah zai taimake ka.

Gwamnati kuwa kiran da zan yi mata shi ne ta sa ido sosai a harkar mawaka domin wasu na yin amfani da mawaka ne kawai don aibata wasu yayin da wasu kuma wakokinsu na gurbata tarbiyyar al’umma ne. Bayan nan kuma ya kamata gwamnati ta rika ba mawaka tallafi sosai sannan ta sa hannu wajen magance matsalar satar fasaha da ya addabi sana’ar.

Sannan kirana a gare ta na karshe shi ne ta sani ana isar mata da sako cikin sauki zuwa ga al’umma kuma cikin hikima. Misali yankin da na fito (Kudancin Kaduna) kowa ya san yanki ne da ya yi kaurin suna wajen rikicin kabilanci da na addini. To kuma kusan dukkanin kabilun da ke yankin babu wacce ba ta da mawakin Hip-Hop. Ka ga a nan gwamnati za ta iya yin amfani da mu domin cusa fadakarwa da kuma yin kira ga zaman lafiya a cikin wakokinmu wanda na tabbata, a cikin matsalolin rikice-rikicen nan guda dari, mawakan Hip-Hop da ke yankin za su iya rage kashi arba’in daga ciki ta hanyar wakokinsu.