✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mawaka sun taimaka a yaki da COVID-19 – Rabiu Dalle

 Rabiu Yakubu, wanda aka fi sani da Rabiu Dalle Lafazi, mawaki ne kuma makadi a masana’antar fim ta Kannywood wanda ya ba da  gudunmawa wajen…

 Rabiu Yakubu, wanda aka fi sani da Rabiu Dalle Lafazi, mawaki ne kuma makadi a masana’antar fim ta Kannywood wanda ya ba da  gudunmawa wajen wayar da kan jama’a game da annobar COVID-19.

A zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilansa na yin haka da ma kalubalen da suke fuskanta a masana’artar fim a lokacin annobar.

Wane ne Rabiu Dalle?

Sunana Rabiu Yakubu, wanda aka fi sani da Rabiu Dalle Lafazin Waka. Ina zaune a garin Kano, ni makadi ne, kuma mawaki a masana’antar Kannywood, wato mawaki na sashen tallace-tallace da aikewa da sako da fadakarwa ga al’umma.

Kuma alhamdulillah a wannan hali da duniya ta tsinci kanta na annobar COVID-19, ni ma ina ba da gudunmawata wajen yin amfani da sana’ata domin fadakar da jama’a game da wannan matsala da ke tunkarar duniya.

Rabiu Dalle Lafazin waka

 

Kasuwar fim ta koma intanet

Alal hakika annobar COVID-19 da Allah ya jarabce mu da ita, aba ce da ta shafi duniya baki daya ba ma kasarmu kadai ba, annoba ce da a baya muke ji a wasu sassa na duniya, daga baya ta shiga ko’ina.

Ta kuma taba masana’antu da dama, kuma duniyar kanta hankalinta a tashe yake ganin yadda wannan annoba ke saurin yaduwa.

Wannan ne ya sanya masana a bangaren lafiya suka ba da shawarwari ciki har da matakin kulle jama’a da aka yi a gida.

To wannan abu ya shafi al’amura da yawa ciki har da tamu sana’ar duk da dai a yanzu sana’armu ta kida da waka aba ce da ke da kasuwa a yanar gizo (intanet) wato tashoshin YouTube da shafukan da mutane ke da su a yanar gizo.

Don haka idan har mutum ya iya aikinsa mai inganci da fadakarwa tare da ilmantarwa da nishadantarwa, muddin ka yi wakokinka, ko shirinka masu inganci ka sanya a kafar intanet, masu so za su je su bibiya domin yanzu lokaci ne na fasahar sadarwa ta zamani, kana daga zaune kudinka za su shiga asusun ajiyarka na banki.

Yadda COVID-19 ke shafar sana’ar fim

Annobar COVID-19 ta shafi aikace-aikacen da muke yi na sana’ar ta fuskar  bukukuwa da daurin aure da sauran tarurruka.

A baya mukan je mu nuna tamu bajintar, a yanzu an dakatar da tarurruka, duk a dalilin wannan annoba.

A baya wata guda zuwa biyu kafin watan azumi za ka ga ana yawan gayyatar mu aiki, a bana babu halin yin hakan, saboda wannan annoba, ba aba ba ce da ake so a tara jama’a.

Amma hakan ba ya hana mu yin aiki a kafafen yada labarai irin gidan radiyo da talbijin da kuma shafukan yanar gizo, domin wannan lokaci ne da muke ba da gudunmuwarmu wajen dakile annobar.

Kuma lokaci ne da muke debe wa jama’a kewa a lokacin da aka kulle su a gida a watannin baya domin kare yaduwar cutar, lokacin da babu maganar yin wasa a sinima ko makamancin haka.

Amma kuma a wani bangaren kuma ita ma Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) tana kiran wasu daga cikinmu ta ba mu aikin fadakarwa.

An yi amfani da wakoki na kallo ko na ji domin a fadakar wa jama’a yadda za su fahimci wannan annoba su kuma kiyaye hanyoyin da take yaduwa.

Rabiu Dalle Lafazi

 

Wakokin kare yaduwar annoba

Akwai wakoki da na yi na kashin kaina domin ba da gudunmuwata ta kare yaduwar cutar.

Sannan akwai wakokin da sauran abokan sana’ata da dama suma suka yi.

An yi wakoki da dama wasu wakokin akwai wadanda suka dauki nauyin su don a yada.

Sannan kuma a karan kanmu mun yi wakoki na kashin kanmu ganin yadda wannan annoba ta yi barna a wasu kasashe da suka fi tamu cigaba inda za ka ji an ce mutum sama da dubu sittin sun mutu a Amurka da sauran kasashe.

Wato abu ne da an dade ba a yi irinsa ba a duniya. Annoba da ta tsayar da dawafi a Harami. Ni tun da nake ban taba gani ba, don haka abu ne da ya tayar da hankalin jama’ar duniya wanda ke bukatar gudunmuwar kowa.

Don haka mun ba da tamu gudunmawar, mun yi wakokin fadakarwa an sanya a kafafen yada labarai da kuma na sadarwar zamani.

Abokan sana’ata irinsu Ali Nuhu, Ali Jita, Nazifi Asnanik, Alan Waka da su Ado Gwanja da sauran mawaka sun ba da irin tasu gudunmuwar.

kalubalen wayar wa ‘yan kasar Hausa  kai

Addu’ar da muka yi ita ce kada Allah Ya sa wannan cuta ta karaso  Kano ko kuma Arewa baki daya, ba don komai ba, ba kuma don mun raina al’ummarmu ba, sai don nauyin fahimta a cikin al’ummarmu.

Muna samun kalubale yadda za a fahimci abu, a yi amfani da ilimi a yarda da shi, a dauki matakin kariya.

Don haka akwai bukatar a dage da wayar wa jama’a kai, kuma da za mu samu tallafi ko masu daukar nauyi to a shirye muke mu kara kwazo da dagewa wajen wayar wa jama’armu kai bisa wannan annoba, musamman a kauyukanmu, domin ko a baya ma ana  maganar kulle ne kawai amma mutane ba sa bin ka’idojinta.

Za ka ga jama’a a cikin unguwanninsu suna ci gaba da harkokinsu yadda suke so.

Amma idan aka ba mu dama za mu yi bakin iyawarmu domin ganin an samu fahimtar wannan matsalar.

Saboda a yanzu akwai wadanda ba su yarda akwai wannan cutar ba, duk da matsalar karuwar mace-mace da aka samu, musamman ma a Kano inda dattijai masu shekaru hamsin zuwa sama ke mutuwa, idan an ba mu dama za mu yi tarin wakoki da za su yi tasiri a kuma samu nasara.