Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da suyi koyi da irin kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW).
Gwamnan, ya yi kiran ne a lokacin da Musulmin Jihar Gombe suka gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).
- Sarkin Gombe zai nada Gwamna Inuwa Yahaya sarauta
- An sako Sarkin Bungudu bayan wata daya a hannun ’yan bindiga
Wannan na kunshe ne a wata takarda da aka aike wa manema labarai mai dauke da sa hannun Daraktan labaran gidan gwamnati Isma’ila Uba Misilli, inda ya hori Musulmi da su yi koyi da darussan da ke cikin watan na maulidi.
Ya bukaci Musulmi su zama masu hakuri da juriya da jajircewa wajen dabbaka kyawawan dabi’u irin na Annabi, sannan su zama jagorori nagari.
Har ila yau gwamnan ya ja hankalin al’ummar Musulmai kan yin juriya da tawali’u da ladabi da karamci, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar a lokacin rayuwarsa.
A karshe ya bukaci a ci gaba da gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaban jihar da kuma kasa baki daya, su kuma jama’a su ci gaba da kasancewa masu bin doka a duk in da suke.