Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce, babu bukatar ya yi yakin neman zabe a 2023, saboda gwamnatinsa ta yi ayyukan da ba a yi tsammani ba.
A cewarsa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yana gogewar da ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba idan suka zabe shi a 2023.
- An kashe fararen hula 17,831 daga fara yakin Ukraine zuwa yanzu – MDD
- An tsinci gawar attajirin Rasha a otel din Indiya
“Muna bukatar ci gaba mai dorewa da karfafawa shi ya sa za mu zabi Tinubu, wanda ya ya yi alkawarin dorawa daga ayyukan alherin Buhari.
“Ina tabbatar muku cewa ba zai ba da kunya ba,” in ji shi, yana mai cewa Shugaba Buhari ya yi ayyuka masu tarin yawa na inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Gwamnan Inuwa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara Fadar Lamidon Gona, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, a yankin Amada a Karamar Hukumar da ke jihar.
Ya bukaci al’ummar masarautar da su zabi Jam’iyyar APC tun daga sama har kasa a zabe mai zuwa.
Ya jaddada cewa APC ce kadai Jam’iyyar da ta damu da halin da ’yan Najeriya ke ciki.