Shugaba Buhari ya yi kira ga ’yan Najeriya da su hada hannu da gwamnatinsa a kokarin da take yi na yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaban ya yi wannan kira ne a sakonsa na Mauludi ga al’ummar Musulmin kasar ta hanyar wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a.
- Buhari ya ziyarci fasinjojin jirgin kasa a asibiti
- ASUU na da hannu a rashawar da ake samu a bangaren ilimi —Buhari
Shugaban ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kula da hakkin mata da yara da kuma girmama su, sannan su rika mutunta juna.
A cikin sakon, Shugaba Buhari ya yi kira ga ’yan siyasa da su guji amfani da miyagun kalamai ga junansu, su kuma guji cin zarafi da mutuncin juna, duk da nufin kaskantar da abokan siysarsu.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Fiyayyen Halitta, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda saboda kyawawan halayensa ne mutane da yawa suka karbi Musulunci.
Daga karshe ya jaddada aniyarsa na tabbatar da an gudanar da zabe mai ingancin da salama a shekarar 2023.