✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsin tattalin arziki na dan lokaci ne —Ministar Kudi

Ministar ta bayyana hakan ne a taron tattalin arziki karo na 26 da aka fara gudanarwa a Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta ce matsalar tattalin arziki da Najeriya ta tsinci kanta a ciki na dan wani lokaci ne.

Hakan ya fito ne daga bakin Ministar Kudi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, a a taron tattalin arzikin kasa karo na 26 da aka fara a Abuja ranar Litinin.

“Matsin tattalin arziki da aka shiga zai kasance na dan wani lokaci ne; masu ruwa da tsaki sun fara aiki tukuru don samar da matakai da za su inganta yanayin”, a cewar ministar.

Taron Tattalin Arzikin Kasa karo na 26, an shirya shi ne da hadin guiwar Maaikatar Kudi, Kasafi da Tsarin kasa (FMFBNP).

Zai ba wa masu ruwa da tsaki a gwamnati da kamfanoni damar yin nazari tare da kawo mafita ga halin da aka tsinci kai musamman yadda annobar COVID-19 ta yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

A ranar Asabar, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar da cewa Najeriya ta sake fadawa kangin koma bayan tattalin arziki.