Gwamnatin Tarayya ta ce matsalar tattalin arziki da Najeriya ta tsinci kanta a ciki na dan wani lokaci ne.
Hakan ya fito ne daga bakin Ministar Kudi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, a a taron tattalin arzikin kasa karo na 26 da aka fara a Abuja ranar Litinin.
- Zanga-zangar #EndSARS ta kassara Tattalin Arzikin Kasa —Minista
- Tattalin arzikin Najeriya ya yi faduwa mafi muni a shekara 10
- Yadda tattalin arzikin Najeriya ya kara tsukewa
- Atiku ya yi takaicin sake karyewar arzikin Najeriya
“Matsin tattalin arziki da aka shiga zai kasance na dan wani lokaci ne; masu ruwa da tsaki sun fara aiki tukuru don samar da matakai da za su inganta yanayin”, a cewar ministar.
Taron Tattalin Arzikin Kasa karo na 26, an shirya shi ne da hadin guiwar Maaikatar Kudi, Kasafi da Tsarin kasa (FMFBNP).
Zai ba wa masu ruwa da tsaki a gwamnati da kamfanoni damar yin nazari tare da kawo mafita ga halin da aka tsinci kai musamman yadda annobar COVID-19 ta yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.
A ranar Asabar, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar da cewa Najeriya ta sake fadawa kangin koma bayan tattalin arziki.