✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsayin tsarkake ayyukan ibada don Allah a Musulunci (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu,…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad, tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. 

Bayan haka, yau ma ga ci gaban mukalarmu ta matsayin ikhlasi a Musulunci. In ba a manta ba, mun kwana a karshen inda muka yi tsokaci kan cewa shi ikhlasin nan don Allah, hanya ce ta sa’ada (daukaka). Mun gabatar da ayoyin da suke nuni a kan haka, saboda haka muna fata Allah Ya sa abin da aka karanta ya yi tasiri don a samu dacewa.

Abin da yake wajibi a Musulunci shi ne ikhlasi
Yawan aikin ibada ba shi ne wajibi ba a Musulunci, abin lura sosai kuma wanda yake tilas shi ne ingantaccen ikhlasi don Allah, to sannan sai a yawaita aikin, wanda shi ma din lallai ya kasance ya yi muwafaka (dace) da sunnar Almusdafa, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ubangijinmu, (Subhaanahu Wa Ta’ala), ya dunkule wannan bukata, gaba dayanta, a cikin fadinSa, Madaukaki, cewa, “Kuma ba a umarce su da komai ba, face bauta wa Allah, suna masu tsarkake addinin gare Shi, masu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsayar da Sallah, kuma su bayar da Zakkah, kuma wannan shi ne addinin wadanda suke a kan hanyar kwarai!” (Albayyinah, aya ta 5).
Sai ga shi wannan ayar ta ikhlasi ta hado da ayyukan tsayar da Sallah da kuma bayar da Zakkah!
Shi aikin ibada, ko da ya kasance mai yawa, matukar babu kyautatuwar kuduri (i’tikaadi), yana gangarar da mai shi ne zuwa ga wuta. Allah Ya kiyashe mu! Shi ya sa ma Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, game da ayyukan kafirai da munafukai, Ya ce, “Kuma Muka gabata zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi kura watsattsiya.” (Alfurkan, aya ta 23).
Dangane da fadin Allah, Mai girma da daukaka, “Shi ne (Allah) Wanda Ya halitta mutuwa da rayuwa domin Ya jarraba ku, Ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawun aiki, Shi ne Mabuwayi, Mai gafara,” (Almulk, aya ta 2), Fudailu bin Iyad ya ce, “(Mutum) ya tsarkake shi kuma ya sadar da shi.”
Sai (dalibansa) suka ce, “Ya Baban Aliyu, mece ce manufar “ya tsarkake shi kuma ya sadar da shi”? Sai ya ce, “Shi aikin ibada, idan ya kasance tsarkakakke don Allah (mai ikhlasi), amma bai sadu (dace) da Sunnah ba, to ba za a karbe shi ba. Idan kuma ya dace da Sunnah, amma babu ikhlasi a cikinsa, shi ma ba za a karbe shi ba, har (sai) ya kasance don Allah (kadai) kuma ya dace da Sunnar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wato shi (aikin) khalis – ya kasance tsarkakakke don Allah; sawab kuma – ya kasance yana kan Sunnah.”

Wadanne ayyuka ne zan yi ikhlasi don Allah a cikinsu?
Wani sashe na mutane suna daukar cewa shi ikhlasi ana yin sa ne kawai a cikin ayyukan Sallah da karatun Alkur’ani da ayyukan ibada na zahiri, kamar addu’a wajen neman wani abu daga Allah da ciyarwa, misali, wannan ba haka maganar take ba.
Shi ikhlasi wajibi ne a cikin dukkan ayyukan ibada, har da ziyartar makwabci da sadar da zumunci da yin biyayya ga iyaye; wadannan duk ana bukatar a yi don Allah kadai, musamman ma da yake suna cikin ayyukan ibada masu girma da martaba da suke dunke al’umma waje guda.
Duk aikin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi, to wajibi ne a tsarkake niyya a cikinsa. Kuma wannan fa, duk yadda aikin ya kasance, karami ne ko babba, domin har a fagen mu’amaloli ya shiga, kamar bukatuwar yin gaskiya a cikin sha’anin cinikayya da kyautata zamantakewar auratayya da kyauta-yi cikin tarbiyyar ’ya’ya da dai abin da ya yi kama da haka, na daga ayyukan ibada. Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Ba ka ciyar da abin ciyarwa ba, alhali kana neman yardar Allah a yin hakan, face an ba ka lada; kuma aikin nan ko da wata loma ce da ka sanya a bakin matarka.” An yi ittifaki kan Hadisin, wato Bukhari da Muslim sun ruwaito shi.
Duk al’amarin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga zance (magana, furuci) da ayyukan da suke bayyane da kuma wadanda suke boyayyu, abin da yake wajibi a cikinsu shi ne yin ikhlasi. Ba a damuwa da kankantar aikin!

Gurabun ikhlasi
Idan tsarkake ayyukan ibada don Allah, Shi kadai, ya yi karfi, yana daukaka ma’abucinsa zuwa ga mafi girman darajoji. Abubakar bin Iyash, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Abubakar Siddik bai shige gabanmu da yawan Sallah ba, bai shige gabanmu da yawan azumi ba. Yadda al’amari yake shi ne shi imaninsa ya tabbata, matukar tabbata, a cikin zuciyarsa, sannan ga sauki da rangwame a cikin dabi’unsa.”
Dangane da wannan ne ma Abdullah bin Mubaarak yake cewa, “Da yawa karamin aiki yake kasancewa mai girma, saboda niyyar da aka gabatar da shi. Haka nan kuma da yawa babban aiki yake kasancewa kankantacce, saboda niyyar da aka gabatar da shi.”
Don haka da aiki karami ko kadan, wanda ya hadu da ikhlasi, sai a samu ninkin-ba-ninki na lada a kansa. Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabino daya daga abin da ya tsuwurwuta (nema) na kyakkyawan abu, – Allah ba Ya karba, sai daga kyakkyawa, – sai Allah Ya karbi abin sadakar da Hannun Dama, sannan ya rika kiwata (habaka) shi don mai shi din, – kamar dai yadda dayanku yake kiwon marakinsa har ya zama bajimi, – har sai abin nan ya zama kamar wani dutse mai girma.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi (an yi ittifaki a kan Hadisin).
Malam Ibnu Kasir, a tafsirinsa, mujalladi na daya, shafi na 317, a cikin fadinSa Ta’ala, “Kuma Allah Yana ribinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani.” (Bakarah, aya ta 261), ya ce, “(Allah) Yana kididdige ikhlasin mai aikin ibada a cikin aikinsa.”
Yana daga cikin kari dai, a kan abin da ya gabata, cewa, idan ikhlasi ya yi karfi, niyyar mutum ta kai matuka wajen tabbata, aikin ibada, wanda aka shar’anta kasancewarsa a boye, ya kasance a boye din, to sai bawa ya zama makusancin Ubangijinsa, Wanda Zai shigar da shi a karkashin inuwar Al’arshinSa, a ranar da babu wata inuwa sai ta Allah.
Da wannan ne ma Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Mutum bakwai, Allah Zai sanya su a cikin inuwarSa… sai ya ambata daga cikinsu, “da mutumin da ya bayar da wata sadaka, ya boye ta, har ta yadda hagunsa ba ta san abin da damarsa ta bayar ba.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Mu kwana a nan, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu, mu ci gaba. Kafin lokacin muna kara rokon Allah Ya kara taimaka mana a cikin wannan tafiya da ake yi ta gudanar da mulkin kasar nan, nan gaba. Allah Ya ba shugabannin nan mataimaka na kwarai.
Wassalamu alaikum warahmatullah!