✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin Mata Game da Ibadar Aure 9

Assalamu Alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu Alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan matsalolin mata game da ibadar aure daga inda muka kwana kafin zuwan watan azumin Ramadana; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Bushewar ‘Yammatanci
Matsalata ta gaba da zamu tattauna daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga uwargida lokacin gabatarwar ibadar aure shine matsalar bushewar ‘yammatanci. (Yammatanci wajene da koda yaushe yake jike cikin lema da danshi), daukewar wannan lema ko karancinta na haifar da matsaloli da yawa ga matan aure musamman lokacin gabatarwar ibadar aure. Bushewar ‘yammatanci na haifar da:
1.    Jin zafi ga uwargida lokacin ibadar aure saboda rashin zubowar ruwan maziyyi da ke rage kaushin goguwar fata da fata da ke faruwa lokacin ibadar aure. Saboda irin raunin da ke tattare da tsokokin da ke cikin ‘yammatanci, rashin zubowar wannan ruwa zai gurjesu, don haka maimakon dadin da a ke sa ran samu sai dai tsananin azabar zafi da za su runka ji. Kuma cigaba da gabatar da ibadar aure akai-akai a cikin wannan yanayi na iya raunatar da yammatanci wata sa’in ma har jini na iya biyo baya.
2.    Rashin samun gamsuwar ibadar aure: Ruwan da ke zubowa a cikin ‘yammatanci mace na kara jin dadin ibadar aure ga duka miji da mata, amma in ya kasance bai zubo ba ko yayi karanci, zai dauke jin dadi gabadaya ga uwargida, sannan ya rage samun gamsuwa ga maigida.
3.    Fargabar Ibadar aure: Wahalhalun da ibadar aure ke haifar ma uwargida a dalilin rashin isashshiyar lema zai sa ta rinka fargabar ibadar aure, wannan fargaba a hankali za ta zama kiyayya, ta ji kwata-kwata ba ta son gabatarwar ibadar aure. Hakan kuma na iya zama sanadiyar yawan fadace-fadace da maigida, musamman in uwargida ta kasa daurewa wajen bashi hakkin shi na ibadar aure saboda wahalar da ta ke sha.
Abubuwan da ke haifar da bushewar ‘Yammatanci: Sinadarin ‘yammatancin nan estrogen shine da alhakin kula da lafiyar ‘yammatanci ta hanyar kiyaye lemarsa, tsaurin tsokokinsa da kuma sinadaran da ke bashi kariya daga kwayoyin cuta. In ya kasance akwai karancin sinadarin estrogen cikin jini wannan shi ke haifar da karancin lema da kuma karancin kariya daga kwayoyin cuta a ‘yammatancin mace.
Abubuwan da ke rage yawan sinadarin estrogen cikin jini sun hada da:
1.    Haihuwa; shayarwa; gabatowar daukewar yin jinin haila da kuma lokacin daukewarsa; shan taba; cutukan da suka danganci garkuwar jikin dan’adam; magungunan cutar sankara da na kaba na mahaifa duk suna rage yawan sinadarin estrogen din dake cikin jini.
2.    Sannan magungunan yaye damuwa na iya haifar da bushewar ‘yammatanci. Haka nan magungunan murar sanyi da kuma magungunan cutukan kyama da kyan jiki (allergies) suna busar da kafofin lemar jiki duka, har da lemar cikin ‘yammatanci.
3.    Haka nan yin amfani da ruwan wanke ‘yammatanci (douching) na wargaza kyakykyawan tsarin da a ka gina ‘yammatanci akai, sai ya kasance an sami karancin lema da karancin kariya da kwayoyin cuta.
4.    Rikirkicewar sinadaran rayi a dalilin yawan fargaba, tsananin huzni, mugunyar gajiya, ko dalilin rashin lafiya ko shan maganin wata cutar. Sannan yawan shan kayan mata, ko hakkin maye na iya haifar da rikirkicewar sinadaran rayin da zai yi tasiri ga lafiyar ‘yammatanci.
5.    Mugunyar gajiya: dabi’antuwa da yawan tara gajiya cikin jiki, rashin kwanciyar hankali, yawan bacin rai da sauran bakaken shau’uka na rage karfin kwararar jini cikin hanyoyinsa, hakan kuma na yin tasiri ga motsuwar sha’awar ‘ya mace, ga shi kuma sai sha’awa ta motsu sosai cikin jiki sannan har ‘yammatancin mace zai zubo da wannan lema mai alfanu ga gabatarwar ibadar aure.
6.    Magungunan tsarin iyali: Wasu daga cikin magungunan tsarin iyali na iya haifar da bushewar ‘yammatanci.  
7.    Cutar da addabi na’urorin sarrafa majina na jiki duka ta kan yi tasiri ga lemar ‘yammatanci.
8.    Rashin gabatar da wasanni kafin ibadar aure na hana zubowar lema a ‘yammatanci lokacin ibadar aure.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Yasa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.