✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin Mata Game da Ibadar Aure (2)

Assalamu Alaikum masu biye da mu, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za…

Assalamu Alaikum masu biye da mu, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. In sha Allah za mu karasa bayanin matsala ta biyu da mafi yawan matan aure suka fi fuskanta game da ibadar aure, da fatan wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Matakan Dawo Da Sha’awa
1. Binciken zuciya: Matakin farko da uwargida za ta bi domin dawo da sha’awarta shi ne, sai ta fara yin tunani mai zurfi game da ita kanta, yanayinta da yanayin halayenta da yanayin sha’awar cikin zuciyarta. Ta yi kokari ta fahimci me ne ne yake tare mata sha’awarta? In da hali ta sami littafi guda ta rubuta dukkanin dalilan da take ganin su ne suke iya rufe mata makunnin sha’awarta, da kuma abin da take ganin zai kawar da su har sha’awarta ta dawo. Na sha fada a cikin wannan fili cewa, ita ’ya mace dole sai jin dadi da kwanciyar hankali da nutsuwar rai dai-dai gwargwadon hali sun saukar mata a zuciya kafin makunnin sha’awarta ya iya kunnuwa sannan ne sha’awarta za ta bude gaba daya. Wasu halaye na nagarta kuma abin so na iya zama cutarwa ga sha’awa, misali: mace mai tsananin hakuri da kau da kai, za a yi ta yi mata abubuwa na cin zarafi amma ta yi ta hakuri tana shanyewa, to wannan shanyewar kala biyu ce, akwai wacce in ta shanye ta shanye ke nan har ga Allah ba za ta kara tunawa da abin ba sai in ta yi dalili. Akwai wacce kuwa za ta kyale ne kawai don ba ta son tashin hankali, ko don jin kai, don tsoro ko don rashin wayo, amma abin yana nan a ranta tana kullace da shi.To irin wannan ’yan kulle-kullen idan aka bar su sai su yi nauyi a zuciya da ruhi, nauyin da zai danne makunnin sha’awa ta yadda ko ya ya aka so a kunno ta ,ba za ta kunnu ba.
2. Tsabtace Ruhi da zuciya: Bayan an kammala wannan bincike don gano abubuwa masu nasaba da zuciya da ruhi da za su iya tare sha’awa, mataki na gaba don dawo da sha’awa shi ne tsabtace ruhi da zuciya ta hanyar:
• Kwance duk wani kulli da yake cikin zuciya; goge duk wata tsatsa da kuma wanke duk wani dattin da yake cikin ruhi da zuciya.
• Tabbatuwa koda yaushe a cikin kyakkyawan hakuri da saurin yafewa da mance laifuka yafiya ta har abada.
• Rayar da kyawawan shauki da tunani a cikin zuciya da yin fatali da duk wani bakin shauki mai nauyaya da sa kunci a zuciya.
• A takaice dai dole sai uwargida ta koyi kasancewa cikin jin dadi da kanta, jin dadin mutanen da take tare da su da kuma jin dadin halin da ta samu kanta a ciki.Wannan shi ne zai haifar da irin nutsuwar da zai bankado da sha’awarta ta dawo kamar da.
3.Daina jin kunyar miji:Idan uwargida tana jin kunyar miji ko kunyar yin ibadar aure da shi, musamman idan kunyar ta yi tsanani, to wannan yana iya nauyayar da makunnin sha’awarta, domin ita kwakwalwa tana fassara duk wani abu da ake jin kunyarsa, da abu mara kyau wanda ranta bai kamata ya yi ba, to don haka sai makunnin sha’awar mace mai tsananin jin kunya ya ki kunnuwa ko ya ya ta so ta kunna shi kuwa. Don haka sai a dage a cire kunya ta fannin ibadar aure. Na san kunya ba ta ciruwa rana daya, amma in aka daura niyya, a hankali, wata rana sai a yi mamakin wai an ji irin wannan kunyar.
4.Magance gajiya: Muguwar gajiya ita ce wacce take yin tasiri ga ma’aikatar hankali har ta haifar da tsananin huzni, da rikirkicewar shaukin cikin zuciya. Muguwar gajiya tana sahun gaba na manyan abubuwan da suke kawo daukewar sha’awar mafi yawa daga cikin mata. Abubuwan da suke haifar da irin wannan muguwar gajiya sun hada da matsananciyar gajiyar gangar jikin dan Adam, kamar matan aure da suke yini kullum cikin ayyukan kula da gida ba dare ba rana.Kullum a gajiye suke kwanciya barci kuma da safe ko barci bai ishe su ba haka za su tashi su ci gaba da gudanar da ayyukan kula da gidanjensu. To irin wannan matsananciyar gajiyar da gangar jiki yake kasancewa a ciki kullum, in ta taru sai ta haifar da mugunyar gajiya mai yin lahani ga ma’aikatar hankali da shaukin cikin zuciya. Haka nan rashin samun isasshen barci akai-akai, da matsananciyar damuwa, faruwar wata mummunar kaddara, rashin samun cikar burin rayuwa, rashin kyakkyawar zamantakewa tare da miji ko abokan zama, duk abubuwa ne da suke haifar da mugunyar gajiya mai yin lahani ga na’urar sarrafa halayyar dan Adam.
Don jin yadda za a magance matsalar muguwar gajiya, sai a biyo bayani mai zuwa sati na gaba in sha Allah; da fatan Allah ya sa mu kasance a cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.