✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin Mata Game da Ibadar Aure 10

Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan matsalar bushewar ‘yammatanci, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Yadda za a magance bushewar ‘Yanmatanci

Abu mafi alfanu da uwargida za ta fara yi wajen kokarin magance wannan matsala shine ta hanyar gano abinda ya haifar mata wannan matsala tun farko, kuma binciken likita ne zai iya tabbatar da musabbabin faduwar ta, don haka sai uwargida ta daure ta je asibiti a yi mata gwaje-gwajen da suka dace don gano ainihin abinda ke damunta da kuma bata irin maganin da ya dace.
Wasu hanyoyi kuma da uwargida za ta bi don samun waraka daga wanna matsala, sun hada da:
1. Cin Kayan Dadi: Mafi yawan lokutta, rashin cin abinci mai kyau, wanda ya kunshi dukkanin sinadaran gina jiki, shi ke haifar da lahani ga ma’aikatar sha’awar ‘ya mace, domin kamar yadda ya gabata cewa abinci shine masarrafin sha’awa: abinci mai kyau  ke haifar da sha’awa mai kyau. Gyara yanayin cin abincin uwargida na iya warware mata wannan matsala ta bushewar ‘yammatanci. Don haka sai uwargida ta fara ta kuma dage da cin lafiyayyen abinci mai karin lafiya, mai bayar da lafiyayyen kuzari kuma mai gina jiki. Wannan ya kunshi dukkan ganyayyaki da ‘ya’yan itace da kayan marmari. Da kuma musamman yawan cin waken suya da dukkan abinda a ka sarrafa da shi, da yawan cin wake da gyada da dangoginsu irinsu gurjiya da sauran su,  domin su wadannan suna dauke da sinadaran da yanayinsu ya zo daya da na sinadarin ‘yammatanci estrogen wanda shine ke da alhakin tabbatar da isashshiyar lema a ‘yammatanci, musamman a lokacin da a ke bukatar kasantuwarta. Da kuma guje ma abubuwan makulashe da tande-tande wadanda sai dai aji dadinsu a baka kadai amma basu ginawa ko bayar da kuzari mai kyau ga jiki. Da kuma guje ma abinci da magunguna masu zuzuta kuzari irinsu goro da shayi mai karfi, domin bayan zuzuta kuzarin da suke yi kuma suna haifar da rikirkicewar sinadaran rayi wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da bushewar ‘yammatanci.
2. Uwargida ta yawaita cin abubuwa masu kara sha’awa da ni’ima a jiki irin su madarar shanu, ruwan tatacciyar kwakwa, zuma, dabino kunun aya da sauran ‘ya’yan itace da kayan lambu da magunguna da a ke hadawa da hakukuwa daban-daban.
3. Yawan shan ruwa: Abubuwa masu dauke da sinadarin caffeine irinsu goro, bakin shayi, coffee, lemun kwalba, lemun karin kuzari, da panadol edtra duk suna tsotse ruwan jiki, don haka in har ya zama dole a yi amfani da su to sai a bi bayan haka da yawan shan ruwa sosai. Jikin dan adam yana bukatar akalla lita daya ta ruwan sha a kullum.
4. Uwargidan ta guji amfani da ruwan sabulun wanke al’aura, (watau douch), yin wanka cikin kwamin wanka, yin amfani da sabulai masu tsananin kamshi da man shafawa na ruwa a ‘yammatanci, domin wadannan duk suna kara busar da cikin ‘yammatanci.
5. A guji amfani da sabulan wanka masu kamshi, ko masu dauke da sinadaran kashe kwayoyin cuta. Da ruwan kumfa da ake sarrafawa musamman don wanke cikin ‘yammatanci: douches’ domin sinadaran da ke cikinsu suna busar da ‘yammatanci kuma su lalata kyakykyawan tsarin da ‘yammantacin ke tafiya akai
6. Wasu kala-kalar kayan da’a da hakkin maye suna saukar da lema sosai a ‘yammatancin ‘ya mace’ wadannan sun hada da irinsu sharkatabu, zummuwar mata; gumbar mata; tukudi, da sauransu.
7. Magance mugunyar gajiya da tabbatar da lafiyar na’urar should, domin mugunyar gajiya na yin tasiri ga lafiyar jiki, sannan bakaken shau’uka suna haifar da rashin lafiyar jiki, don haka sai mace mai fama da wannan matsala ta binciki kanta, zuciyar da kwakwalwarta, duk wasu abubuwa marasa dadi da ta daddale cikin zuciyarta ta sama masu mafita, ta hanyar rubuta dukkan damuwarta a cikin wani dan littafin sirri, ko ta hanyar tattaunawa da wani aminiyarta, wannan zai sa ta fitar da dukkan damuwarta kuma ta yi ma abubuwan  damuwarta kallo ta wata mahanga daban, wacce zai sa ta samu kyakykyawar fahimta game da su, hakan zai sa su zama ba su damunta a zuciyarta kuma.
8. Yawancin mata suna bukatar wasanni da maganganu masu dadi kafin gabatarwar ibadar aure domin haka zai motso da sha’awarsu, hakan zai motsar da na’urar da zata jika cikin ‘yammatancinsu da lema, rashin wadannan wasanni da kalamai da kauna na iya haifar da bushewar ‘yammatanci lokacin ibadar aure. Don haka sahihin maganin wannan matsala ga wasu matan shine sai mazan aurensu su runka daurewa wajen daukar lokaci mai tsawo suna masu wasanni da kalaman kauna ta yadda sha’awarsu za ta motsu sosai har a samu zubowar wannan lema mai muhimmanci.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.