✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin da suka hana samuwar ’yanci ga kananan hukumomi

Daya daga cikin cikas da gazawa da aka samu a yayin gyaran Kundin Tsarin Mulki, shi ne yadda aka kasa samun daidaito da nasarar sama…

Daya daga cikin cikas da gazawa da aka samu a yayin gyaran Kundin Tsarin Mulki, shi ne yadda aka kasa samun daidaito da nasarar sama wa kananan hukumomin kasar nan ’yancin cin kashin kansu. Kuma ba kowa ne ya dakile wannan yunkuri ba sai gwamnonin jihohi tare da hadin bakin majalisun jihohinsu. Kamar yadda abin ya faru, ya zuwa yanzu dai, an samu majalisun jihohi 23 cikin 36 da ake da su a kasar nan, wadanda suka nuna rashin amincewa da ba kananan hukumomi cin gashin kansu. Sai dai duk da wannan mataki da suka dauka, bai kamata a yi sanyi ba, domin kuwa dakile ’yancin kananan hukumomi tamkar murkushe dimokuradiyya ne, ganin cewa kananan hukumomi ne ke kusa da mafi yawan al’ummar kasa.
An dauki lokaci ana batun nema wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu a Kundin Tsarin Mulkin kasar nan, amma abin takaici ga shi a wannan karon ma an kasa cin ma nasara. Babu shakka ya kamata a sake dawo da tattaunawa game da batun, domin kuwa kananan hukumomi suna da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman ma saboda irin ayyukan da suke gudanarwa, ganin cewa su ne suka fi kusa da jama’a.
kananan hukumomi suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa yankunan karkara, kamar yadda kowace gwamnati da haka take bugun gaba. Sai dai a zamanin nan, abin ba haka yake ba, kasancewar yadda aka bar yankunan karkarar a lalace, babu wani abin ci gaba.
Kundin Tsarin Mulki ya tanadar masu da ayyukan da hakkoki na musamman, kamar kuma yadda aka tanadar masu irin kason kudinsu daga asusun kasa. Amma sai ga shi ana dakile haka, aka yi masu shinge ga dukiyarsu. Ta haka ne gwamnoni ke fakewa da Asusun-Hadin-Gwiwa, suna hana kananan hukumomin ’yancin tafiyar da kudadensu yadda ya kamata. Ana barin su da ’yan kudi kalilan da ba su wadatar da su, balle su gudanar da nauye-nauyen ayyukan ci gaba ga al’ummarsu.
Mafi yawa daga gwamnoni sun yi ta hakilo, har suka ja ra’ayin takwarorinsu tare da ’yan majalisun tarayya, wajen ganin cewa sun hana kananan hukumomin ’yancin cin gashin kansu, a lokacin da aka zo batun yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima.
Gwamnoni sun rika nuna cewa, ayyukan da Kundin Tsarin Mulki ya ba kananan hukumomi, su ma suna da ’yancin gudanar da su. Ga shi an kwashe shekaru 14 ana gudanar da mulkin dimokuradiyya amma har yanzu gwamnonin ba su sakar wa kananan hukumomin mara ba, suna ci gaba da rike dukiyarsu.
Wani abin dubawa kuma shi ne, mafi yawa daga shugabannin kananan hukumomin, sun kasa jajircewa su bi kadin hakkokinsu, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanadar masu. Wani abin misali shi ne, akwai wani sabon tsari da ya fayyace al’amuran dauka da gudanarwar ma’aikatan kanannan hukumomi da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi kuma ta amince da a aiwatar da shi, amma har yanzu ba a fara aiwatarwa ba, saboda dakile shi da gwamnatocin jihohi da suka yi.
Wannan matsala ta baya-baya da ta samu kananan hukumomi, ya nuna cewa lallai akwai bukatar a samu sabbin hanyoyin da za a bi domin ganin an sama wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kansu. Namijin kokarin da Majalisar Tarayya da kuma Makarantar Koyar Da Ayyukan Majalisa suka yi na sama wa kananan hukumomi karsashi, abin yabawa ne, sai dai hakan ba zai wadatar ba har sai an gyara Kundin Tsarin Mulki, ta yadda zai bayyana karara ’yancin cin gashin kan kananan hukumomi.