✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Sarkin Mutum Biyu ya umarci a yi rajistar baki

Sarkin Mutum Biyu da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba, Alhaji Sani Suleiman Duna ya ce zai dauki mataki a kan duk wani hakimi…

Sarkin Mutum Biyu da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba, Alhaji Sani Suleiman Duna ya ce zai dauki mataki a kan duk wani hakimi ko dagaci da mai unguwa da suka bari masu aikata laifuffuka suka zauna a yankunansu

 Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin kungiyar Raya Masarautar Mutum Biyu wanda aka yi a garin Mutum Biyu kwanakin baya.

Sarkin ya ce saboda matsalar rashin tsaro ya zama tilas masu sarautun gargajiya wadanda su ne iyayen kasa su sa ido a kan bakin da suke shigowa yankunansu.

Alhaji Sani Suleiman wanda Sarkin ne Mai daraja ta Biyu a Jihar Taraba ya bayar da umarnin cewa daga yanzu dole ne hakimai da dagatai da masu unguwani su rika yi rajistar duk bakon da ya shigo yankinsu domin gudun bai wa masu aikata laifuffuka matsugunni.

Sarkin ya ce zai sa kafar wando daya da duk wani hakimi ko dagaci da mai unguwa da ya ki yi wa baki rajista a masarautarsa.

Ya ce bayan yi wa baki rajista kuma dole ne a sa ido a kan duk wani bako da ya shigo domin gane halaye da dabi’unsa.

Sarki ya ce masu aikata laifuffuka na kwararowa yankunan karkara a sassan jihar suna sajewa da jama’a kuma daga baya su rika aikata miyagun ayyuka.

Ya ce ana samun aukuwar satar mutane da fashi da makami da hallaka bayin Allah a wasu yankunan masarautarsa inda ya ce dole ne hakimai da dagatai su sa ido domin kawo karshen matsalolin tsaro a yankunansu.

Ya sharwarci iyaye a masarautar su taimaka wajen shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi da matasa ke yi a yankin, ya ce yawan aukuwar laifuffuka na faruwa ne a dalilin shan kwayoyi a tsakanin matasa.

Alhaji Sani Suleiman ya kuma yaba wa iyayen yara da suke bai wa ’ya’yansu karfin gwiwa wajen neman ilimin zamani da na addini. Ya ce wannan zai taimaka wajen bunkasa ilimi a masarautar Mutum Biyu. 

An tara sama da Naira miliyan bakwai ga Gidauniyar Bunkasa Ilimi da Ci Gaban Masarautar ta Mutum Biyu.