Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na samun galaba a yunkurinta na magance matsalolin tsaro, inda ya ce yanzu matsalar raguwa take ba karuwa ba.
Shugaban ya kuma kalubalanci kafafen yada labarai da su dada taimakawa wajen kawo karshen matsalar ta hanyar rahotannin da suke yadawa.
- Najeriya A Yau: Yadda Aka Kashe Mutum 65 A Goronyo
- Jiragen yaki Super Tucano 12 da Buhari ya sayo sun iso Najeriya
Buhari na wadannan kalaman ne a cikin sakonsa na bikin Mauludi na bana domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W.).
A cikin wata sanarwar da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar ranar Litinin, Shugaban ya ce, “Lokaci ya yi da za mu canza maganar ‘karuwar matsalar tsaro’ da ‘raguwar matsalar tsaro’.”
Shugaban ya ce la’akari da yadda sojoji da ’yan sanda da ma sauran jami’an tsaro suke aiki tukuru wajen ragargazar ’yan ta’adda a kasar, matsalar tsaro na dab da zama tarihi.
Buhari ya kuma ce, “Ina farin cikin mika sakon gaisuwar zaman lafiya, hadin kai da fatan alheri ga al’ummar Musulmi, sauran ’yan kasa da dukkan Musulman duniya saboda bikin Mauludi,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga Musulman kan su dage da neman gafara da kokarin kwaikwayon salon rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W) wanda ake bikin ranar haihuwar tasa.