Jam’iyyar NNPP ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus daga mukaminsa cikin gaggawa saboda gazawarsa wajen samar da tsaro a kasar.
Shugaban jam’iyyar reshen Jihar Katsina, Sani Liti, ne ya yi wannan kiran yayin ganawa da manema labarai a birnin Dikko ranar Litinin.
- LABARAN AMINIYA: Barazanar Tsaro Ta Janyo Rufe Makarantun FGC A Abuja
- Sarkin Kano ya sabunta lasisinsa na tuki
Liti ya ce, batutuwan da suka shafi rashin tsaro da suka hada da karuwar talauci, sun ci gaba da karuwa musamman saboda rashin shugabanci nagari da kuma lalacewar tattalin arziki wanda ya haifar da tsadar rayuwa ga al’umma.
“Gwamnatin Buhari ba kawai ta yi kasa a gwiwa ba ne wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya, kamar yadda ya yi alkawari, amma ta jefa kasar cikin kangin talauci saboda cin hanci da rashawa.
“Idan har shugaban kasa ya yi jinkirin yin murabus, to muna bukatar Majalisar Dokokin kasar da ta yi amfani da hanyoyin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada domin ceto rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
“Za a tuna cewa daga 2015 zuwa yau, sama da ‘yan Najeriya 50,000 ne suka rasa rayukansu a sakamakon ta’addancin ‘yan bindiga.
“Haka kuma, an yi asarar kadarori na maduden kudade da kuma kudin fansa ga ‘yan ta’addan da suka yi amfani da kudin wajen siyan makamai kamar yadda wasu ‘yan fashin suka yi ikirari,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kafa dokar ta-baci kan harkokin tsaro, inda ya ce, “A dangane da haka, muna kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar sojojin haya na tsawon watanni shida daga ko’ina domin yakar ’yan bindiga, da masu tayar da kayar baya da kuma masu rura wutar kabilanci.
Kazalika, ya kamata gwamnati ta gaggauta daukar matasa ‘yan Najeriya miliyan daya da za a horas da su a matsayin runduna ta musamman da za ta kare da kuma tabbatar da tsaron kasar.
Shugaban ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-baci a jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara da Neja da kuma Sakkwato, tare da rufe asusun ajiyarsu ta yadda za a yi amfani da duk wasu kudade domin kare jihohin daga ‘yan bindiga da suka addabe su.
“Idan har Gwamnatin Tarayya ta ki daukar mataki, muna rokon dukkan Majalisun Dokoki na jihohi su fara ayyukan tsige gwamnoninsu,” in ji shi.