Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya ce duk da matsalar tsaron da ake fuskanta, ba za a kwatanta halin da ciki da na da ba.
Janar Lucky, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron ibada na musamman a coci domin tunawa da ranar ’yan mazan jiya, ya ce kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta na dab da zama tarihi.
- A wajen dan sanda na sayi bindiga saboda na rika kare kaina – Matsafi
- Najeriya A Yau: AFCON 2021: Tana Kasa Tana Dabo
Ya ce, “Ina so in mika jinjinata ga dakarun sojoji, musamman zaratan cikinsu, wadanda suka kafa harsashin da muke gini a kansa domin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane sashe na Najeriya.
“Tabbas akwai tarin kalubale, amma bai kai na lokacin da muka fara aiki ba. Hakan na ba da kwarin gwiwar cewa a wannan sabuwar shekarar akwai alamun haske kenan.
“Akwai babbar damar ci gaba da amfani da yanayin da ya samar da zaman lafiyar da muke da shi yanzu ya dore, ta yadda babu wanda zai sake zama cikin taraddadi a kasar nan,” inji Babban Hafsan Tsaron.
Shi ma a sakonsa na fatan alheri, Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce ana shirya taron ne a kowacce shekara domin tunawa da ’yan mazan jiya da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hadin kai da ci gaban kasa.
Ya ce akwai sojoji da dama da suka rasu a yakin duniya na daya da na biyu da na basasa, da aikin samar da zaman lafiya a wasu kasashen da kuma yaki da ta’addanci, ’yan bindiga da kuma ’yan aware da ma sauran barazanar tsaro.
Janar Faruk ya ce ba za a taba mantawa da irin gudunmawar da suka bayar ba, sannan ya yi addu’a ga wadanda suka mutu.
Ya kuma ce ci gaba da kula da wadanda suka samu raunuka abu ne da zai ci gaba da zama a kan gaba a kudurorin rundunar da ke karkashinsa.