Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana matsalolin tsaron da suka addabi kasar a matsayin babban kalubalen da ke fuskantar rundunar ’yan sandan kasar.
Shugaban ya bukaci manyan jami’an rundunar da su yi nazari akan matakan da ya dace su dauka domin kare lafiya da dukiyoyin jama’a.
- Zama kwararre a hada bidiyon bincike a wata 2
- Kisan Malcom X: Za a biya mutanen da aka daure diyyar $35m
Buhari ya yi wannan kira ne yayin da yake bude taron manyan hafsoshin ’yan sandan a Jihar Imo a ranar Litinin.
Shugaba Buhari ya kuma janyo hankalin manyan jami’an ’yan sanda wajen kaucewa goyan bayan wata jam’iyya, yana mai cewa shirin da suka yi ne zai nuna yadda za su tabbatar da ganin an gudanar da zaben shekara mai zuwa cikin lumana.
Buhari ya ce an kashe makudan kudade wajen samar da tsaro da kuma shirya zabe mai zuwa, saboda haka babu dalilin da zai sa a bari wasu bata gari su hana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Buhari ya ce jami’an ’yan sandan ne za su jagoranci samar da tsaron da ake bukata wajen samun karbabben zabe a kasar.
Kazalika, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bai wa ’yan sandan goyan bayan da suke bukata tare da kula da ma’aikatan hukumar.
Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na gudanar da karbaben zaben da duniya za ta amince da shi a shekara mai zuwa.