✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Jam’iyyar ADP ta bukaci Majalisa ta tsige Buhari

Sani, wanda shi ne tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar ta ADP, a ranar Talata ya ce gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawuran da…

Shugaban jam’iyyar Action Democratic Party (ADC), Injiniya Yabagi Y. Sani, ya bukaci majalisa ta tsige shugaban kasa Muhamamdu Buhari, saboda gaza kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

Sani, wanda shi ne tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar ta ADP, a ranar Talata ya ce gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawuran da ta daukar wa ‘yan kasar.

“Matsalar tsaro ita ce babbar matsalar gwamnatin Buhari, don haka majalisa ya kamata ta fara shirin tsige shi daga kujerarsa.

“Ta ya za a yi shugaban kasa ya kasa bayyana a gaban majalisa a kan abin da ya shafi rayuwar al’umma?

“Su wa shugaban kasa yake wakilta? Sannan me yasa majalisa ba za ta yi wani abu a kai ba? Majalisa ba ta yi aikinta ba a nan.

“Manyan hafsoshin tsaro sun gaza, misali duba irin yadda ta faru a Amurka, mutane sun tsige Trump duk da cewar har yanzu yana ofis, amma sun sauya shi.

Ya ci gaba da cewa kowa a jam’iyyarsu ta ADP na da damar tsaya wa takarar shugabancin kasar nan.

Sannan ya kara da cewa jam’iyyar ta su ta ADP ba ta amince da tsarin karba-karba daga bangororin Najeriya ba.

“Ba mu damu da cewa ko kai Bahaushe ne, ko kuma Banufe bane, matukar za ka yi abin da aka zabe ka don shi, to magana ta kare.

“Don haka ba mu da wani tsari na karba-karba, sai da za mu tabbatar da duk wanda zai tsaya takara zai yi abin da al’umma suka zabe shi don shi,” a cewar Sani.