✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: Dalilin da muke neman hadin kan kasashe —CDI

Idan ba a tashi an farga ba Najeriya za ta daina wanzuwa saboda matsalar tsaro.

Shugaban Sashin Tsaro na Sirri a Najeriya (CDI), Manjo Janar Samuel Adebayo, ya ce akwai bukatar samun hadin kan kasashen waje, domin kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin taron shekara-shekara na masu ba da shawara kan tsaro wanda Hukumar Leken Asiri ta (DIA) ta shirya.

Da yake jawabi, Adebayo ya ce idan har aka cimma wannan muradi, za a samu sauki wajen wuce gona da irin da kungiyoyin ’yan ta’adda ke yi ta hanyar amfani da alakarsu da sauran ’yan ta’addan da ke ketare wajen mallakar muggan makamai da samun sauran tallafi.

A cewarsa, wannan lamari na samun tallafi ’yan ta’adda ke yi daga takwarorinsu na ketare ya zamo barazana ga Najeriya, wanda ya tilasta wa kasar neman hadin kan kasashe domin ci gaba da wanzuwa.

A nasa bangaren, Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin tsaro, Babagana Monguno ya ce baya ga samun hadin kan kasashe, akwai bukatar yankunan kasar su hada kai, domin saukaka wa sojoji ayyukansu na kawo karshen ta`addanci.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin taron an kuma kaddamar da na’urorin zamani masu saukaka ayyukan tattara bayanan sirri.