✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: Buhari ya kira taron gaggawa

Amurka ta kwashe wasu daga cikin jami’an diflomasiyyarta da iyalansu da ke Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi taron gaggawa da manyan jami’an tsaron kasar a Abuja a ranar Litinin.

Wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce taron zai mayar da hankali ne kan yadda za a karfafa matakan tsaro a sassan kasar.

Taron zai wakana ne kwanaki kadan bayan da Amurka ta fitar da wata sanarwa da ke kashedin cewa akwai yiwuwar aukuwar hare-hare a wasan sassan Najeriya, ciki har da Abuja babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce, Amurkar ta kwashe wasu daga cikin jami’an diflomasiyyarta da iyalansu da ke Abuja.

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce suna daukan matakan da suka dace wajen ganin sun dakile duk wata bazarana da ka iya tasowa.

Najeriya, wacce ita ce kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka, na fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram a Arewaci da kuma matsalar ‘yan aware a Kudanci, ko da yake mahukuntan kasar sun ce lamarin na lafawa.