✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: An ƙone uwa da jaririyarta ƙurmus a Sakkwato

Ta kone ne bayan ’yan bindiga sun bude wa motar da take ciki wuta

Wata uwa mai suna Sharifa Noma da jaririyarta sun ƙone ƙurmus a Jihar Sakkwato.

A cewar wasu majiyoyi, matar ta haihu ne wajen misalin ƙarfe 2:30 na daren Talata.

“Bayan haihuwar, ta yi ta zubar da jini, wanda hakan ne ya sa iyalanta suka yanke shawarar kai ta asibiti domin duba lafiyarta,” in ji majiyar.

Sai dai bayanai sun nuna a kan hanyar zuwa asibitin ne sai motar da suke ciki ta daki wani shinge da ’yan bindiga suka kafa a kan hanyar Ruwa Wuri zuwa Bugawa da ke Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar.

Daga nan ne sai ’yan bindigar suka bude wa motar wuta, inda direbanta ya rikice, hakan ya sa motar ta kwace ta daki bishiyar, kuma ta kama da wuta.

“Direban da uwar da kuma ɗaya daga cikin jariran nata sun ƙone,” kamar yadda mahiyar ta ƙara.

Shi ma wani mazaunin yankin da ya ce sunan shi Kabiru, ya ce sauran fasinjojin da ɗaya daga cikin jariran marigayiyar sun tsira da rayukansu a lamarin.

Sai dai ya ce sun sami raunuka, kuma yanzu haka suna can suna samun kulawa a asibiti.

Da muka tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Ahmad Rufa’i, bai tabbatar da labarin ba, saboda ya ce har yanzu bai samu bayanai ba a kai.