Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin Arewa maso Yammacin kasar a matsayin lamarin da ya kai mataki na intaha.
Yayin wata hira da ya yi a safiyar Alhamis da gidan Talabijin na Arise dangane da halin da kasar nan take ciki, Shugaban ya ce tura ta kai bango dangane da rahotanni na matsalar tsaro da ke fitowa daga yankin Arewa maso Yamma.
Shugaban ya ce matsalar tsaro na ci gaba da faruwa a yankin duk da fadi-tashi gami da nasarorin da rundunar sojin kasar ke samu wajen tunkarar lamarin.
A cewarsa, “tura ta kai bango dangane da halin tsaro a yankin Arewa maso Yamma kuma wadannan mutane masu ala’adu iri daya su ne suke kashe junansu kuma suke satar shanu a tsakaninsu.
“Lamarin a halin yanzu ya kai intaha, amma za mu magance shi nan ba da dadewa ba. Ba kuma za mu ci gaba da yayata lamarin ba amma tabbas muna samun nasarori domin alamu na nuna cewa an kusa murkushe su.
“Mun tura karin ’yan sanda da sojoji da su yi duk wata mai yiwuwa wajen tsare rayuka da dukiyar al’umma a yankin.
Shugaban kasar ya kara da cewa, gwamnatinsa “za ta tafiyar da duk wasu masu kawo hargitsi a kasar da yaren da suka fi fahimta.”
“Gwamnoni da suka fito daga yankin sun sha kawo min korafi da koke a kan halin da Jihohinsu ke ciki na fama da matsalar tsaro, sai dai abun dubawa a nan shi ne bai kamata jama’a su zabi mutum a matsayin shugaba ba kuma ya nade hannayensa yana jiran komai sai Gwamnatin Tarayya ce za ta yi.
“Dole ne Gwamnoni su tashi tsaye su kulla mu’amala da mutanen da suke jagoranta wadanda suka san duk wani lungu da sako a yankunansu kamar yadda aka rika yi a baya, saboda haka idan jami’an tsaro sun tashi aiki sai lamarin ya zo musu da sauki.”
Shugaban kasar ya ce matukar ana samun wadatattun bayanan sirri daga dukkan masu ruwa da tsaki a jihohin da lamarin ya shafa sannan kuma ana tattaunawa domin samun mafita, da kuwa matsalar da ake fama da ita ba ta kai girman haka ba.
Babu shakka ’yan bindiga na ci gaba da kara kaimi wajen kai hare-hare a Jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato da Zamfara da ke Arewa maso Yammacin kasar.