✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar da ke tattare da sartse

An dai san duk abin da aka rubuta zai samu mutum ba shakka sai ya faru.

A yau za mu duba matsalar sartse ne. Sartse shi ne shigar wani tsinke cikin fata. Mukan kira shi da sunan splinter a likitance.

Yawanci akan samu ne wani dan karamin tsinke ko wani dan bangare na katako ko icce ko karmami su shige cikin fata.

Matsalar sartse matsala ce da ta zama ruwan dare domin kusan ba wanda zai ce bai taba yin sartse ba.

A mafi yawan lokuta matsala ce karama wadda da an cire tsinken shi ke nan, amma a wasu lokutan idan ba a cire tsinken ba kuma ba a je an sa magani wurin ba, to wurin zai iya zama ciwo babba.

Sartse zai iya samun kowa amma ya fi samun masu amfani da wadancan abubuwa da aka lissafa a sama, kuma ya fi faruwa a tafin hannu ko na ’yan yatsu.

Masu aikin shara ko masu yawan shara (har da matan gida) su suka fi yawan samun sartse da tsinken tsintsiya; kafintoci kuma su suka fi samun sartse daga tsinken katako; masu faskare kuma su suka fi samu daga itace; manoma kuma su suka fi samun sartse daga karmami.

Yadda abin ke faruwa kuwa shi ne – idan akwai wani dan karyayyen tsinke a jikin abin da mutum ya kai hannu saitin wurin sai a yi rashin sa’a ya shige fata ya karye.

Zai iya shiga can ciki zai kuma iya shiga waje-waje. Idan waje-waje ne ba a jin zafi sosai sai dai a dan ji kaikayi.

Amma idan can ciki ya shige, za a ji zafi da ma watakila ganin fitar jini. Da zarar hakan ta faru ya kamata a tsaya cak a natsu tukuna a ga ina sartsen ya shiga, ina ya tafi, lumewa ya yi ko a sama-sama yake.

Idan a sama-sama yake, a yi maza a zare tsinken sai a wanke wurin. Idan jini ya fita sai a dan saka maganin kashe kwayoyin cuta a wurin, kamar ruwan iodine ko spirit shi ke nan.

Idan aka kasa cirewa da hannu za a iya sa abin yankan farce a gwada cirowa da shi. Idan ba a ci sa’a ba ya lume cike to sai an je asibiti an ciro shi da wani dan karfe, don kada ya zama babban ciwo.

Kada a ce za a sa allura ko reza domin za su kara girman ciwon ne da saka zubar jini.

Yaya za a kiyaye aukuwar sartse?

An dai san duk abin da aka rubuta zai samu mutum ba shakka sai ya faru, amma ga wadanda suke yawan samun sartse musamman wadancan mutane da aka lissafa a sama dole su rika daukar matakan kariya a wurin aikinsu.

Babban matakin kariyar kuwa shi ne ta sa safar hannu mai kwari yayin aiki da wadancan abubuwa da tsinkayensu ke sa sartse.