Gwamnatin Zamfara ta umarci kungiyoyi masu zaman kansu da su tattara kayansu su bar jihar nan take.
Sanarwar korar da Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Ibrahim Mamman Tsafe, ya sanya wa hannu ta zargi kungiyoyin da hannu a matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Gwamnatin jihar ta ce ta lura da yadda kungiyoyin da ba na gwamnati be ke kara kwararowa cikin jihar, inda suke aiwatar da ayyukan da ba su dace ba, wadanda suka saba wa dokokin Jihar.
“Yawancin wadannan kungiyoyi masu zaman kansu ba su yi rajista da gwamnatin jihar nan ba kamar yadda aka shimfida dokoki da ka’idojin gwamnati.
“An kuma gano wasu daga cikinsu da aikata ta’asar da ke haifar da rashin tsaro a jihar da ma makwabtanta, daga yanzu gwamnati ta umarci duk wasu kungiyoyi masu zaman kansu a jihar nan da su tattara kayansu su fice nan take.
“An umarci ma’aikatun gwamnati da su katse kowace irin alaka da duk wata kungiya mai zaman kanta, domin za a dauki matakin hukunta duk wanda aka samu yana da alaka da su.
“Hukumomin tsaro da ke jihar bisa wannan sanarwar, an umarce su da su sanya ido ga kungiyoyi masu zaman kansu, su gudanar da bincike tare da gurfanar da duk wata kungiya da ke aiki a jihar ba tare da izini daga hukumomin da aka tanadar ba.”