Matatar Mai ta Ɗangote da ke Legas ta fara fitar da tataccen man fetur a karon farko a ranar Talata.
Da yake sanar da hakan, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce samar da tataccen man fetur daga matatar abin murna da alfahari ne ga duk ɗan Najeriya.
Ɗangote ya ce, “Da zarar mun kammalan abubuwan da suka rage da Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), man fetur ɗinmu zai ahiga kasuwa.”
Matatar Ɗangote mai karfin samar da ganga 650,000 na tataccen mai a kullum ta fara fitar da fetur ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalarsa da kuma fargabar tashin farashinsa.
- Mutane 87 Boko Haram Ta Kashe a harin Mafa —Mazauna
- Zanga-zanga ta ɓarke kan wahalar man fetur
- Yadda NNPCL ya gwara kan ’yan Najeriya kafin ya gaskata cewa yana biyan tallafin mai
Ɗangote wanda shi ne mamallakin kanfanin ya ba wa ’yan Najeriya “tabbacin samun man fetur mai inganci, wanda zai taimaka wa ababen hawa injinanda ke amfani da shinsu ui ƙarko.
“Ba zai lalata inji ba, wanda shi ne matsalar da yawancin masu ababe ke fama da ita.
“Ingancin fetur ɗinmu zai yi gogayya da na Amurka da ma na ko’ina a faɗin duniya
“Kuna za mu ci gaba da jajircewa wajen ganin ba a fi mu ingancin mai ba,” in ji Aliko Dangote.
A watan Disamban 2023 ne matartar da attajirin ya gina a kan Dala biliyan 20 ta fara aiki.
A watan Janairu ta fara samar da tataccen man dizel da na jirgin sama, kuma ana sa ran zuwa ƙarshen shekarar nan za ta riƙa aiki a cikakken ƙarfinta.