Karamin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri ya shiga tsakani da nufin sasanta rikicin da kunno kai tsakanin Matatar Mai ta Dangote da Kamfanin Mai Na Kasa (NNPCL).
Al’amura su dagule a makon jiya ne, inda aka rika nuna wa juna yatsa tsakanin kamfanin NNPCL da mai Matatar Dangote kuma babban attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote.
A wani taron ’yan jarida daya kira a Legas, Dangote ya yi zargin kusoshin gwamnati da kamfanonin mai na kasashen waje na yi wa matatarsa zagon kasa, ta hanyar hana ta samun danyen man da za ta tace domin samar da fetur.
Bayan nan ne Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, ya bayyana cewa babu kashin gaskiya a zargin da Alhaji Aliko Dangote ke yi.
- Lithium: EFCC ta kama tireloli 3 na ma’adinan hada jirgin sama na sata
- Matatar Dangote: Ku zo ku saya ku yi yadda kuka ga dama —Dangote ga NNPCL
Shugaban na NMDPRA ya bayyana wa ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa cewa ko lalsisin fara aiki Matatar Dangote ba ta da a shi sannan ba a kammala ta ba.
A cewarsa, matatar ba ta kai matakin kaddamarwa ba, sannan ,an dizel da take sanarwar bai kai wanda ake shigo da shi Najeriya daga ƙasashen waje ba.
Don haka ya ce Najeriya ba za ta dogara da man din Dangote ba, yana mai zargin dan kasuwan da neman kame kasuwancin ɓangaren man ƙasar shi kadai.
Amma a martaninsa, Alhaji Aliko Dangote, ya ce zargin ba shi da tushe, kuma idan NNPCL tana so, zai iya sayar mata da Matatar Dangote, ita ta gudanar da shi yadda take so.
Da hakan ta kawar da shi a matsayin mutum guda da ke neman juya akalar bangaren man.
Daga bisani, Dangote ya shaida wa Kwamitin Wakilai cewa man dizel dinsa matatar ke samarwa na da matukar inganci.
Sannan ya bukaci majalisar ta gudanar da bincike kan zargin rashin ingancin man dizel dinsa domin gano gaskiya.
Wannan dambarwa da ta dabaibaye matatar mai mafi girma a Afrika kuma dunkulalliya ta biyu mafi girma a duniya ya haifar da ce-ce-ku-ce.
Musamman yadda ake tunanin matatar mai karfin samar da tataccen mai ganga 650, 000 za ta taimaka wajen kawo saukin matsalar mai a Najeriya.
A kan haka ne Karamin Ministan Mai, Heineken Lokpobiri, ya gakira ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin samun hadin kai da kuma shawo kan matsalar.
Masu ruwa da tsakin sun hada Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari.
Sauran su ne Shugaban Hukumar MNDPRA, Farouk Ahmed da kuma takwaransa na Hukumar Hako Danyen Mai ta kasa (NUPRC), Mista Gbenga Komolafe.