Majalisar Wakilai ta bukaci a gaggauta dakatar da Shugaban Hukumar Albarkatun Mai Na Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, kan dambarwar hukumar da Matatar Man Dangote.
Dan Majalisar, Esosa Iyawe, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban na NMDPRA har sai majalisar ta kammala bincike kan zargin almundhana da ake wa a hukumar na ba da lasisi ga kamfanonin da ke shigo da man dizel mara inganci Najeriya daga kasashen waje.
Honorabul Esosa Iyawe ya ce dakatar da shugaban na NMDPRA na da muhimmanci saboda katobarar da ya yi, cewa man dizel din da Matatar Dangote ke samarwa ba shi da inganci idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi daga kasashen waje.
Honorabul Esosa Iyawe ya kara da cewa, “zargin da ake wa NMDPRA na bayar da lasisi ga masu shigo da man dizel mai dauke da sinadarin Sulphur fiye da kima zuwa Najeriya da kuma amfani da shi a kasar babban hadari ne ga lafiyar al’umma, da kuma asara a bangaren tattalin arziki.
- Sau 8 aka aura min ’yan Boko Haram —Ɗalibar Chibok Mai Juna-biyu
- Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
“Katobarar shugaban na NMDPRA, wanda tuni bincike ya ƙaryata, ya fusata ’yan Najeriya, har suna zargin jami’in da yin zagon kasa ga matatun mai na cikin gida.
“Yadda ya dage cewa a ci gaba da shigo da mai daga kasashen waje zangon kasa ne ga tattalin arzikin kasa.
“Sannan gwajin da aka gudanar ya nuna man da ake shigowa da shi na dauke da sinadari (Sulphur) da ke da hadarin gaske fiye da kima ”, in ji shi kamar yadda kafar The Nation ta ruwaito.
Ana iya tuna cewa a wata tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, Farouk Ahmed, ya yi zargin cewa man dizel din Matatar Dangote na dauke da sinadarin Sulphur da ya haura 1,200ppm, na kasashen wajen kuma bai haura 650ppm ba.
650 shi ne adadin Sulphur da NMDPRA ta kayyade wa matatun cikin gida a Najeriya zuwa shekaraer 2025, kamar yadda kungiyar ECOWAS ta kayyade da nufin rage fitar da gurbataccen hayaki da kuma kare muhalli.
Sai dai sakamakon gwajin da aka gudanar kan man dizel din da Matatar Dangote da na kasashen wajen ya nuna ingancin na Dangote sa zarce na kasashen waje nesa ba kusa ba.
Sakamakon gwajin ya nuna Sulphur din man dizel din Dangote 87.6ppm ne, a yayin da samfurin na kasashen waje biyu da aka auna ke dauke da 1,8000ppm da kuma 2,000ppm.
Majalisar Wakilai na daga cikin wadanda suka sanya ido a kan binciken da aka gudanar kan samfurin man dizel din na Dangote da na kasashen waje.
Honorabul Esosa ya ce idan har babban jami’in gwamnati zai yi irin wannan katobarar ba tare da bincike ba, akwai alamar rashin kwarewa da kuma rashin kishin kasa, musamman a halin da ake ciki a Najeriya a halin yanzu.
Dan Majalisar ya ja hankalin abokan aikinsa cewa duk makamashin da ke dauke da Sulphur wanda ke fitar da bakin hayaki sosai musamman daga man dizel, yana haddasa cutar kansa da cutar huhu sannan yana lalata injina da kuma gurɓata muhalli.
Shi ya sa kasashen duniya ke daukar tsauraran matakai don rage adadinsa sosai, ta hanyar yin dokoki da ke wajabta wa masana’antu yin injina da makamashi mai karancinsa domin kare lafiyar jama’a da kuma muhalli.