Wani magidanci ya bukaci kotu ta raba aure tsakaninsa da matarsa da ta haifa masa ‘ya’ya uku, bisa zarginta da auren wani jami’in dan sanda a asirce a kan aurensa.
Saheed Adewoyi ya yi bayanin ne yayin da yake yin ma’an da bukatar matar tasa da suka shekara 12 tare, cewa Kotun Kwastomari da ke zamanta a Ibadan ta raba auren nasu, bisa zargin yana musguna mata.
Magidancin ya shaida wa kotun cewa ‘yan sanda a caji ofis din Eyeleye sun shiga tsakani suka sa Mariam da daduron nata wanda dan sanda ne suka yi alkawari a rubuce cewa ba za su kara cin amanarsa ba, amma ba su daina ba.
Ya ce sakamakon haka ne aka sauya wa daduron matar tasa wurin aiki zuwa caji ofis din Ogbere, amma kuma sai lalatar tasu ta kara kankama har suka je aka daura musu aure a kan aurensa ba tare da saninsa ba.
“Ina jiran Mariam ta dawo gida da yamma sai wani dan sansa ya shaida min cewa ta bi wani dan sanda sabon zuwa dakinsa.
“Da na bi sawu na gano gidan sai na iske su suna tsaka da fasikanci.
“Har mari na mai gidan ya yi, amma daga baya da ya gane cewa matata ce dan sandan yake aikata masha’a da ita a cikin gidan da ya ba dan sandan haya sai ya ba ni hakuri.
“Na kai wa DPO din caji ofis na Testing Ground kara inda dan sandan ke aiki; da DPO ya yi alkawarin kafa kwamitin ladabtarwa a kan wanda ake zargin sai jami’in ya nemi in yafe mishi; har na roki DPO ya kyale shi.
“Sakamakon haka ne aka mayar da daduron nata caji ofis din Ogbere, amma sai alakar tasu ta kara karfi har suka je aka daura musu aure ba da sanina ba.
“Ban san yawancin abubuwan da take aikatawa ba saboda yawancin lokuta takan ce min za ta yi tafiyar kasuwanci ne, wani lokaci har na mako guda.
“Da muka bincika wayarta sai muka gano hotuna da bidiyon bikin daurin aurensu da sunan Ade mi, Ife mi (Kambina, abin kaunata)”.
Magidancin ya gabatar wa kotun hotunan da bidiyon da takardar alkawarin daina cin amanarsa da wadanda yake zargin suka rattaba wa hannu a matsayin hujjoji.
“Ya Mai girma Mai Shari’a, Mariam ta amsa cewa sau uku ta zubar da cikin da dan sandan ya yi mata, kuma an taba kulle shi saboda tsiyatakun fasikancin da suke yi”, kamar yadda Saheed ya shaida wa kotun.
Da farko dai Mariam din ce ta kai kara kotun tana neman a raba aurenta da Saheed wanda take zargi da yawan azabtar da ita.
“Saheed na yawan zargin ina soyayya da wani dan sanda sabon zuwa alhali kuwa kyakkyawar mu’amala ce kawai tskanina da ‘yan sandan caji ofis din Testing Ground saboda kwastomomina ne masu sayen yadi a wurina.
“Wata rana ina cikin jinin al’ada har tsirara ya yi mini, wai yana so ya ga inda nake boye kudi a jikina”, a cewarta ga kotu.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Odunade ya ce auren matar da mijinta ya samu matsalar da raba su ba shi da makawa domin hana zalunci.
Daga nan ya katse igiyar auren, ya damka wa Saheed ‘ya’yan, ya kuma umarci tsoffin ma’auratan da su guji hulda da juna.
Alkalin ya bayyana abin da matar ta yi a matsayin karuwanci kuma abin kunya ga danginta.
Daga nan ya bukaci iyaye da su tarbiyyantar da ‘ya’yansu a kan jin tsoron Allah ta yadda ba za su zubar musu da kima a idon jama’a ba.