Wata matashiya mai shekaru 20 ta shiga hannun ‘yan sanda bisa zarginta da ƙona matar ɗan uwanta da ke naƙuda da tafasasshen ruwan zafi.
A tattaunawarta da Aminiya, matashiyar ta ce ɓacin rai ne ya kai ta ga ƙone matar lokacin da musu ya kaure a tsakaninsu.
- Jirgin Max Air ɗauke da fasinjoji 59 ya tsallake rijiya da baya a Kano
- Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS?
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a garin Dubeli da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa da ke Jihar Adamawa.
Mijin matar da aka ƙona ya ce yana shago ne inda yake sana’a aka kira shi a waya cewa an watsa wa matarsa ruwan zafi lokacin da take naƙuda.
Kazalika ya nuna takaicinsa na sanin ‘yar uwarsa ce ta aikata ta’asar, kuma jim kaɗan bayan hakan ne matar tasa ta haihu.
A nasa ɓangaren, Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nguroje ya tabbatar da kama matashiyar da ake zargin, ya kuma ce za su ci gaba da bincike kafin miƙa ta kotu.