Wata matashiya mai suna Jumoke Kehinde ta kashe kanta ta hanyar shan maganin kashe kwari bayan an dakatar da ita a wurin aikinta saboda zuwa a makare.
An samu gawar matashiyar mai shekaru 23 a jajibirin ranar sabuwar shekara a dakinta da ke Unguwar Kajola a jihar Ondo, wacce ke aiki a wani sanannen kanti da ke birnin Akure.
Mai kula da sanannen kantin da bayar da sunansa a matsayin Taiwo, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa an dakatar da Jumoke da wasu abokanan aikinta saboda laifin da suka aikata na zuwa a makare.
Sai dai Taiwo ya bayyana mamakinsa dangane da yadda matashiyar ta yanke wa kanta wannan danyen hukunci wanda bai taba tsammani ba.
Ya ce, “A ranar da wannan abun al’ajabi ya faru, Jumoke ta zo aiki kamar yadda ta saba a koda yaushe fuskarta cike da annuri, amma daga bisani ta kama gabanta bayan ta karbi wasikar dakatarwa daga aiki da misalin karfe 11 na safe.”
“Da misalin karfe 4 na Yamma, muka samu kiran neman agajin gaggawa wanda aka labarta mana cewa Jumoke ba ta jin dadi sai daya daga cikin ma’aikatanmu ya hanzarta domin amsa wannan kira.”
“An yi kicibus da Jumoke ta yi warwas a kasa a dakinta tana rawar sanyi kuma bakinta na warin maganin kashe kwari wanda haka ya sanya aka garzaya da ita asibiti cikin gaggawa amma kafin wani dan lokaci ta ce ga garinku nan.”
Wani abokin aikin marigayiyar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce bayan an ba Jumoke wasikar dakatarwar, sai ta koma gida ba tare da ta nuna wata alamar za ta kashe kanta ba.
Ya ce “Tabbas mun san cewa duk wanda ya zo aiki a makare za a dakatar da shi na tsawon wasu ’yan kwanaki domin a hukunta shi game da laifin da ya aikata, amma ban ga dalilin da zai sa wannan lamari ya sanya ta kashe kanta ba.”
Yayin da aka nemi jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar, Mista Te-Leo Ikoro, ya ce ba a kai ga shigar musu da rahoton faruwar lamari a caji ofis ba.