Rundunar ‘yan sanda a Legas ta kame wani matashi da ya yi bidiyon kansa a lokacin da yake sumbatar yarinya ‘yar shekara uku.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta ce matashin mai suna Adeyeye Oluwatosin Babatunde dalibi ne a Jami’ar Jihar Legas amma mazaunin garin Shagamu a jihar Ogun.
Kakakin Rundunar Bala Elkana ya ce karamar yarinyar da matashin ke sumbata a bidiyon kwanwarsa da suke uba daya da ita.
‘Bidinyon da matashin ya dauka a ranar 2 ga watan Yuni, 2020 ya karade kafafen sada zumunta ya kuma kawo cece-ku-ce duba matsalar cin zarafin kananan yara da kuma yi musu fyade da ake fama da su.
- Za a yi daurin rai da rai ga masu fyade a Osun
- Fyade: Kotu ta tsare dan shekara 57 da ya lalata yarinya
- An tsare tsohon soja saboda ‘yi wa ‘yar shekara 4 fyade’
“Hakan ta sa Kwamishina ‘Yan Sandan Jihar Legas Hakeem Odumosu ya sa a yi bincike kan bidiyon tare da tsare wanda ake zargin, wanda aka kama a ranar 5 ga watan Yuni.
“Ya yaba wa ‘yan Najeriyar da suka ankarar da rundunar game da bidiyo, yana mai cewa dole ne a hada kai domin yakar cin zarafin yara da mata.
A nasa bangaren wanda ake zargin Adeyeye Oluwatosin ya ce bai yi hakan ba da nufin cin zarafin yarinyar.
“Kanwata ce na saba wasa da ita, mahaifina da mahaifiyarta suna zaure tare da mu a wajen da aka dauki bidiyon.
“Na sumbace ta ne sai na yi bidiyon na sa a ‘status’ dina na ‘WhatsApp.’
“Can sai wata mata ta yi min magana ta WhatsApp din cewa ni mai yin fyade ne. Na ce mata, yarinyar kanwata ce kuma ai ta san ta domin na kan sa ta a ‘status’ dina.
“Ban farga ba, ashe ta sauke bidiyon tana ta yadawa cewa na ci zarafin yarinyar, har abin ya karade intanet.
Ya zuwa yanzu, rukumar ‘yan sandan jihar Legas ta fitar da lambobin kar -ta-kwana guda 10 na tuntubar ta da zarar an ga wani da ake zargi da cin zarafin yara ko mata.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da hankulan jama’ar Najeriya ke komawa kan masu aikata laifin fyade a fadin kasar.