✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ya kashe matar babansa ya kashe kansa a ofishin ’yan sandan Nasarawa

Ana zargin wani matashi dan shekara 23 da rayuwa Ahmed Abdullahi ya kashe kansa a ofishin ’yan sanda da ke Jihar Nasarawa. Matashin wanda aka…

Ana zargin wani matashi dan shekara 23 da rayuwa Ahmed Abdullahi ya kashe kansa a ofishin ’yan sanda da ke Jihar Nasarawa.

Matashin wanda aka fi sani da suna Abba, an kama shi ne da zarginsa da kashe kishiyar mahaifiyarsa a Unguwar Agyaragu da ke Jihar Nasarawa.

Wata majiya ta ce, Ahmed Abdullahi (Abba) ya kashe kansa ne a ofishin ’yan sanda a sashen binciken manyan laifuka wato CID da ke kan titin Makurdi a cikin garin Lafiya a ranar Alhamis na makon jiya.

Majiyar ta kara da cewa, ana zargin cewa shi marigayin ya kashe kansa ne bayan da ya yi ta buga kansa da bangon kankaren inda ake tsare wadanda ake zarginsu da aikata laifi kafin a gurfanar da su a gaban kotu, wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

An dai yi jana’izar Abba ne da daren alhamis da ta gabata.

Aminiya ta ruwaito yadda aka kama Abba da zargin kashe kishiyar mahaifyarsa da wuka, inda ya yanke ta kafa, ta ruga da gudu don neman taimako a gidan makwabta, amm ya bi ta ya ture ta ya kuma yi mata yankan rago wanda ya yi sanadiyar rasuwarta.

Wani na kusa da dangin marigayin ya ce mahaifinsa ya rasu shekaru uku da suka wuce, sannan yana yin aikin achaba da mashin, daga nan ake dargin ya fara shana kwayar zakami da wasu kwayoyi, wanda hakan ya sa ya aika wanan aika-aika.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, ASP, Ramhan Nansel ya ce za su yi karin bayani dangane da rasuwar matashin.