Wani matashi mai shekaru 28 daga Jihar Yobe, Sa’idu Abdulrahman, na shirin shiga kundin tarihin na Guinness, a matsayin gwarzon mai ɗaukar hoto na duniya.
Sa’idu Abdulraham ya ɗauki hotuna 897 a cikin mintuna 60 domin doke wanda ke riƙe da kambun Guinness a wannan bangare a halin yanzu.
Hotuna 897 da ya ɗauka a cikin mintuna 60, sun zarce na Gwarzon Kundin Tarihi na Guinness na yanzu da hotuna 897.
Mai riƙe da kundin na yanzu ya samu matsayin ne bayan da ya ɗauki hotuna 500 cikin mintuna 60.
- Harin bom ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin sojoji da al’ummar Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Rawar Da Fassara Ke Takawa Wajen Haɓaka Harshen Hausa
Abdulraham ya yi ɗamarar kafa wannan tarihi ne bayan bajintar da ya nuna a gaban jami’an gwamnatin Yobe da dalibai da kuma masu hannu da shuni a ranar laraba, 25 ga Satumba, 2024, a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke jihar.
Matashin ya ce ya samu wannan nasarar ne bayan ya shafe watanni 12 yana shirye-shirye, kuma yana fatan samun karɓuwa a daga mahukunta Kundin Tarihi na Guinness.
“Na dauki hotuna 897 a cikin sa’a ɗaya, wanda ya wuce burinmu na 600 duk da ƙalubale da yawa,” in ji shi.