✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi wa ’yar shekara 85 Fyade

Wani matashi dan shekara 29 mai suna Kehinde Ariyo ya shiga hannun ’yan sandan Ilesa a Jihar Osun, bayan da ya yi wa wata tsohuwa…

Wani matashi dan shekara 29 mai suna Kehinde Ariyo ya shiga hannun ’yan sandan Ilesa a Jihar Osun, bayan da ya yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 85 fyade, har sai da ta suma.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Mista Fimihan Adebayo ne ya gabatar matashin ga manema labarai, inda ya bayyana cewa Ariyo ya yi wa matar fyade ne har sai da ta galabaita, ta suma har sai da aka kai ta asibiti ta farfado. Ya ce tsohuwar ta samu raunuka sosai a sakamakon wannan fyade amma yanzu ana kan ba ta magani, tana samun sauki. Ya kara da cewa da zaran sun kammala bincike, za su gurfanar da matashin a kotu.

Wakilinmu ya tattauna da matashin, wanda ya bayyana cewa, da dare ne yana dawowa daga fati sai ya ji barci ya kama shi. Kan haka sai ya je gidan wannan tsohuwa, ya roke ta da ta ba shi wurin kwana, kafin da safe ya wuce, kuma ta amince. 

“Da dare sai na je dakinta na ce ina son in fada mata wani abu, na ce mata ta bude dakin nata. Bayan ta bude, daga nan ba zan iya tuna abin da ya faru ba. Na san dai na yi jima’i da ita sau biyu kuma wannan aikin Shaidan ne,” inji matashin.