Dan wasan ninkaya na Nijeriya mai suna Akinrodoye Dare, ya yi ninkayar kilomita 11.8 a gadar ‘Third Mainland’ a Tekun Legas a wani yunkuri na ja hankalin jama’a kan illar mutum ya kashe kansa da kansa.
Dare da ake kira ‘Coach Dreh’ ya bai wa mutane da yawa mamaki yayin da ya shiga cikin ruwa tun daga farkon tekun a yankin Oworonshoki ya ƙare a tashar motoci ta Adeniji Adele.
Ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu da minti 33 yana ninkaya lamarin da ya ɗauki hankalin jama’a a shafukan sada zumunta.
A hira da manema labarai, dan wasan ya bayyana gamsuwa da ninkayar da ya yi, yana mai cewa ya yi ta ce don wayar da kan jama’a game da matsalolin lafiyar kwakwalwa, musamman kan yadda ake samun wasu suna kashe kansu ko yunƙurin yin hakan bayan sun samu kansu a cikin damuwa.
Matashin ya bayar da labarin tashin hankalinsa a rayuwa, wanda ya kusan kai shi ga rasa rai, amma al’ummar da ake samu masu ninkaya suka kai dauki suka dakile kisan kansa da ya yi niyya ta hanyar fadawa kogi.
“Hakan ya faru a kaina inda wasan nikaya ya ceci rayuwata, wanda ba don agajin da na samu ba da tuni na mutu.
“Lokacin da na soma wasan ninkaya, na yi dangi da ’yan uwa. Babu shakka wasan ya ceci rayuwata.
“Akwai kuma wani abokina da ya riƙa tunanin kashe kansa, amma mun gode wa Allah da aka shawo kan al’amura kuma muna buƙatar a kawo ƙarshen irin wannan yunƙuri domin akwai mutane da dama da suke tunanin daukar ransu,” in ji shi.
Dangane da zaɓin gadar ‘Third Mainland’ don soma ninkayar ya ce, alkaluma sun nuna cewa mutane da dama sun kashe kansu a kan wannan gada ko sun yi yunƙurin haka a kan gadar da ke tsakiyar teku, don haka ya yi amfani da wannan wurin a matsayin misali.
Ya nanata cewa tunanin kashe kai yana tasiri a zukatan masu yin haka, don haka ya yi kira ga mutanen da suka samu kansu a cikin ƙunci, su daina ɓoye lamarin.
“Su dinga magantuwa da kuma bayyana halin da suke ciki ga jama’a don samun dauki.
“Daya daga cikin abin da nake so in yi nuni kansa hi ne, ga al’ummarmu ina son mu saurara da kyau domin mutanen da suke kashe kansu suna da nasu hanyar sadarwa.
“Don haka akwai bukatar jama’a su lura sosai da wadanda suka yi yunƙurin ɗaukar ransu, muna gaya musu su daina yin shiru, kawai ku fito ku faɗi damuwarku.
“Ba ma son su kashe kansu kuma mutane na yin bakin ciki a duk lokacin da haka ya kasance,” in ji shi.
Ya alaƙanta iyon da ya yi a matsayin mafi daɗewa tun bayan zamansa dan wasan ninkaya inda ya kwashe sama da shekara goma, yana mai nuni da wannan bajintar ga horo da tallafi daga bangarori masu zaman kansu da na gwamnati.
“Shekarun da na yi na samu kwarewa a wasan ninkaya sun wuce shekaru goma, kuma zango mafi tsayi da na yi ninkaya a ruwa shi ne mai nisan kilomita 10, amma a wannan karon na yi ninkaya nisan sama da kilomita 11.8,” in ji shi.
Tekun Legas a yankin gadar ‘Third mainland’ ko gadar Babangida, ya yi ƙaurin suna inda mutane masu son ɗaukar ransu suke zuwa su faɗa ciki har da wata mace wadda daga baya aka gano ma’aikaciyar DSS ce da ta fito daga mota ta yi tsalle ta faɗa cikin teku daga kan gadar a shekarar 2023.