✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi garkuwa da mahaifiyar budurwarsa

Ayarin ’yan sanda daga ofishin Sufeto Janar sun kama wani matashi dan shekara 24 bisa zarginsa da shirya garkuwa da mahaifiyar budurwarsa inda ya amshi…

Ayarin ’yan sanda daga ofishin Sufeto Janar sun kama wani matashi dan shekara 24 bisa zarginsa da shirya garkuwa da mahaifiyar budurwarsa inda ya amshi kudin fansa a Karamar Hukumar Ukwa ta Yamma da ke Jihar Abiya.

Matashin mai suna Chinindu Innocent, kamar yadda ’yan sanda suka bayyana, ya hada kai ne da wadansu mutum uku, suka  sace matar. Wadanda aka kama tare da matashin sun hada da Ekendu Chidiebere da Tochukwu Samuel da Ikechukwu Nwankwo.

’Yan sanda sun ce mutanen sun ki yarda su sako matar da suka yi garkuwa da ita, har sai da suka amshi kudin fansa na Naira dubu 300 daga iyalanta. An yi zargin cewa, tun farko sun nemi a biya su Naira miliyan shida ne kafin su sako ta amma daga bisani suka rage kudin zuwa Naira dubu 300.

Innocent da tawagarsa an kama su ne sakamakon wata takardar koke da aka aike wa Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, kan yadda aka sace matar mai shekara 50. Daga nan sai Sufeto Janar din ya ba Kwamandan Ayarin IRT, Mataimakin Kwamishina Abba Kyari umarnin ya binciko wadanda ke da hannu ko ake zargi da aikata laifin.

Kakakin ’Yan sandan Najeriya, Moshood Jimoh ya tabbatar da kama wadanda ake zargin kuma sunan hannun masu bincike a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja. Ya ce bincikensu ya gano cewa Innocent saurayin ’yar matar da suka yi garkuwa da ita ce kuma ya amsa cewa ya aikata wannan laifi. Ya ce kishin budurwar tasa ne ya jefa shi ga aikata wannan laifi.

Ya ce, “Matar da muka kama ita ce mahaifiyar budurwata kuma na hadu da ita ce sanadiyyar sana’ar da suke yi ta cajin batirin wayoyi. Nakan je gidansu inda suke wannan sana’a, ina cajin wayata. Ta haka ne har na zama kamar amininsu, kuma na fara soyayya da daya daga cikin ’ya’yan matar.”

“Bayan mun yi ’yan watanni muna soyayya da juna, sai na fahimci cewa budurwar tawa tana soyayya da wani. Lokacin da na tuntube ta da maganar, sai ta bata rai, har ma ta yi mini barazanar cewa za ta daina soyayya da ni. Wani dan uwana ne ya ba ni shawarar wannan mataki da na dauka, ta kama mahaifiyarta domin amsar kudin fansa. Ya ce mini wani daga cikin abokansa mai suna Onyenya ya samu dukiya saboda wannan sana’a ta garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da yake yi,” inji shi.