Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, sun kama wani matashi mai shekaru 25, kan zargin sace wani yaro ɗan shekara biyu a duniya, Al’amin Ahmad Garba, tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 50.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 25 ga watan Disamban 2024.
- ’Yan bindiga sun kashe sojojin kamaru 6 a kan iyakar Najeriya
- Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota
An gano yaron a wani gida da ke unguwar Dorayi bayan ya shafe kwanaki uku a ɓoye.
Bayan an ceto yaron, an kai shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad don duba lafiyarsa, sannan aka miƙa shi ga iyayensa.
An gurfanar da wanda ake zargin a kotun majistare mai lamba 25 da ke Nomansland, a Kano.
Kakakin ya ce matashin yanzu haka yana tsare a hannun hukuma, yayin da ake ci gaba da shari’a.