Wani matashi ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar shan fiya-fiya saboda an karbe takarar shugabancin karamar hukumar Rimin Gado daga hannun wanda yake mara wa baya.
Matashin ya sha fiya-fiya ne a daren ranar Litinin da nufin huce haushin da ke damunsa kan tsayar da dan takara a jam’iyyarsu ta APC.
- Ganduje zai dauki malamai 2000 aiki a Kano
- Saudiyya za ta raba rigakafin COVID-19 kyauta
- Muhimman abubuwa kan dan Najeriyar da ya kirkiro rigakafin COVID-19
Ya ce ya zabi yin hakan ne saboda ya huce bakin cikin da aka sanya masa na canza wanda suka zaba a matsayin dan takara.
Ya ce da aka zo zaben fidda gwani, an zabi Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Garba Shu’aibu Rimin Gado a matsayin wanda zai sake tsayawa.
“An yi zabe kuma ya samu kuri’u 35 cikin 43 da aka kada, amma wasu suka zagaye suka zuga gwamna ya kwace takarar.
“Da farko fa gwamnan ya amince da a ba shi takarar amma kawai aka koma aka zuga shi ya karbe ya ba wani daban.
“Kuma abin haushin ma shi ne wadanda suka fi cin dunduniyarmu, su ne suka rika yakar gwamnan a lokacin zaben da aka yi na baya-bayan nan”, inji shi.
Da yake mayar da martani kan yadda lamarin ya faru, dan uwansa ya ce, an kira shi cikin dare aka fada masa ga halin da dan uwansa ke ciki.
Bayan ya je wurin sai suka dauke shi zuwa babban Asibitin Rimin Gado domin ba shi taimakon gaggawa.
Da aka yi masa allurai sai aka tura su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin ci gaba da duba lafiyarsa.
Ya kara da ce wa bayan ba shi dukkanin taimakon da ya dace tuni aka sallame su suka koma gida inda yake ci gaba da samun lafiya.